kungiyar Mahauta da Dillalan Dabbobi sun koka game da rufe Kasuwar Shanu da Jami’an tsaro suka yi a garin Maiduguri makonni uku da suka gabata, a sakamakon zargin da ake yi na sayar da dabbobi ba bisa ka’ida ba.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Alhaji Abubakar Bula ya ce kungiyarsu ba ta ji dadin yadda jami’an tsaro suka yi wa kasuwar dirar mikiya saboda wani dalili na daban.
“A gaskiya ba mu ji dadin yadda jami’an tsaro suka rufe wannan kasuwar ba yau makonni uku ke nan. Hakan ya haifar da asarar fiye da naira miliyan 100. Har ila yau, akwai mutane kusan miliyan biyu da suka rasa abinci daga wannan kasuwar,” inji shi.
Ya ce kamata ya yi a ce jami’an tsaro su yi bincike a tsakanin ’yan kasuwan ko za a gane wani mara gaskiya mai hada kai da Boko Haram suna kawo dabbobi ko kuma ana sayarwa da Boko Haram din dabbobi saboda haka ana iya samun ba ta gari a cikinmu domin wake daya shike data gari, ya ce don haka muke so jami’an tsaro su yi bincike su tabbatar da mai gaskiya, “idan kuma an kama mai laifi to mu mun yarda a hukunta shi idan ya so a bar mu mu bude kasuwarmu,”
Ya ce kasancewar mutane masu cin abinci a kasuwar a yanzu sun koma suna gararanba a gari.
Bugu da kari, ya ce “nama ya yi karanci a gari don haka muke rokon jami’an tsaro da gwamnatin tarayya da ta Jihar Barno, da su yiwa Allah su bude mana wannan kasuwa domin mu ci gaba da neman abincinmu.’’
Daga nan shugaban ya bukaci ’yan kasuwa da su kasance masu bin doka da oda musamman lokacin da jami’an tsaron za su gudanar da bincike a kansu domin zakulo marasa gaskiya, “domin wajibi ne idan muna son ci gaba a harkar wannan kasuwar mu bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai da goyon baya don cimma burinmu na sake bude wannan kasuwa,” inji shi.
kungiyar Mahauta ta koka kan rufe kasuwa a Barno
kungiyar Mahauta da Dillalan Dabbobi sun koka game da rufe Kasuwar Shanu da Jami’an tsaro suka yi a garin Maiduguri makonni uku da suka gabata,…