✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar kwadago ta yi watsi da sdabon karin farashin man fetur

Kungiyar ta ce babu ta inda karin zai amfani talakan Najeriya

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ta yi fatali da karin farashin man fetur zuwa N617, inda ta ce hakan na iya kara jefa ‘yan Najeriya cikin tsaka mai wuya.

Da yake martani game da karin, babban jami’in yada labarai da harkokin jama’a na kungiyar na kasa, Kwamared Benson Upah, ya bayyana cewar karin na iya zama babbar barazana ga rayuwar al’umma da tattalin arzikin ‘yan kasa.

Kazalika, ya ce karin farashin zai shafi sana’o’in jama’a, hanyar kudaden shiga da kuma yadda ake gudanar da rayuwarsu.

NLC ta shaida wa Gwamnatin Tarayya da ta janye shirin da ta ke na ninka farashin nan fetur zuwa Naira 1,000 kan kowace lita.

Ya ce kungiyar ba ta gamsu cewar cire tallafin zai iya taimaka wa jama’a ko tattalin arziki ko kuma yadda zai sake sabunta rayuwar jama’a ba.

Ya ce, “Wannan karin ba za mu amince da shi ba saboda zai iya haifar da babbar barazana ga zamantakewa da tattalin arzikin kasa, kasuwanci, kudaden shiga da kuma rayuwar al’umma!.

“Mun sha fada cewa babu wata gwamnati da za ta yi aiki da hankali, ta bar harkokin kudi ga hannun ‘yan kasuwa ba saboda hakan na iya haifar da sakamakon mara dadi.

“Sabon farashin man fetur yana nuna cewa farashin na iya tashi zuwa Naira 1000 ko sama da haka a kowace lita nan ba da jimawa ba.

“Muna bai wa gwamnati shawara ta janye daga wannan shiri. Jama’a ba su ji dadin wannan ci gaba ba. Bai kamata a dauki hakurin mutane da wasa ba,” in ji shi.

Da safiyar ranar Talata ne aka wayi gari litar man fetur ta tashi daga Naira 540 zuwa Naira 617 a birnin tarayya Abuja, yayin da a Jihar Kano litar man fetur din ta kai Naira 620.