✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar man fetur: ′Ba mu zabi Tinubu don ya dada kuntata mana ba′

Mutumin ya koka kan mawuyacin halin da talakawa ke ciki a yanzu.

Adamu Salihu, wani mazaunin Babban Giji a yankin Karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, ya koka da yadda aka wayi gari farashin man fetur ya haura Naira 600, inda ya ce ba don haka suka zabi Tinubu ba.

Ya yi gargadin cewa matukar abubuwa suka ci gaba da karuwa kamar haka, lamarin zai iya jefa mutane da dama su fada ta’addanci a kasar.

A ranar Talata ce aka wayi gari farashin man fetur ya kai Naira 617 a gidajen mai na NNPC da ke Kano da ma wasu sassan Najeriya.

Sai dai Salihu, wanda dan asalin Karamar Hukumar Bichi ne a jihar, ya bayyana hakan ne don nuna bacin ransa game da karin farashin man fetur da aka yi daga 540 zuwa 620.

Ya ce “Gaskiya wannan sabon farashin ya jefa mu cikin tsaka mai wuya. Wannan ba shi ne abin da muka zabi gwamnati ta mana ba. Ana mana sabanin abin da muka bukata.

“Dan Najeriya ne, kuma ina bukatar a martaba ni. Ni ba matashi bane a yanzu, ina da yara kuma dukkansu sun fita sun yi zabe. Idan har ba a samu canji ba zan fada musu su daina zabe kuma za mu zama ‘yan ta’adda saboda ba za su iya ci gaba da zuwa makaranta ba saboda sun fara sayar da awara.

“Na sa sun daina zuwa makaranta kuma yanzu awara suke sayarwa. Ta ya za su kasa samun ilimi su koma sayar da awara. Na dade a siyasa tun zamanin NRC da SDP.

“Idan abubuwa suka ci gaba a haka za mu dauki mataki idan har ‘yan majalisarmu da wakilanmu suka kasa yin komai. Za mu iya daukar doka a hannumu duk da cewar ‘yan kasa ne masu bin doka.

“Duk wannan wahalhalun da muke sha na faruwa ne saboda karin farashin man fetur, idan ba don haka ba ba zamu ke shan wahala haka ba. Ba mu da shugabanci nagari.”

Aminiya ta ruwaito cewar man fetur da ake sayarwa Naira 540 sakamon cire tallafin man fetur, an wayi gari ya koma Naira 620 da safiyar ranar Talata.