Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta janye yajin aikin gargadi na kwana biyar da ta fara a Jihar Kaduna.
Shugaba NLC, Ayuba Wabba, ya sanar da hakan ne bayan zaman gaggawan da suka yi a Kaduna kan kayyatar da Gwamnatin Tarayya ta yi musu domin tattaunawa tsakaninsu da Gwamnatin Jihar Kaduna.
- Gwamnatin Tarayya za ta gana da El-Rufai da NLC
- Gwamnatin Tarayya ta shiga rikicin ’yan kwadago da El-Rufai
- Zan daure shugabannin Kwadago shekara 21 –El-Rufai
Kakakin NLC, Nasir Kabir, ya ce an dakatar da yajin aikin ne a ga abin da zaman da gwamnatin za ta yi da bangarorin a safiyar Alhamis zai haifar.
Ana sa ran ma’aikatan Jihar za su koma bakin aikinsu daga ranar Alhamis, a Jihar Kaduna, bayan sun shafe kwana uku ana kai ruwa rana tsakaninsu da Gwamna El-Rufai, wanda ya ce babu gudu, babu ja da baya a sallamar ma’aikatan da ta yi.
Gwamnatin Tarayya ta gayyaci bangarorin domin tattauanwa da su bayan alamu sun nuna yajin aikin gargadi na kwana biyar da NLC ta fara ranar Litinin a Jihar na neman rikidewa zuwa na gama-gari.
Ta ce za ta “Mininstan Kwadago da Ayyuka, Dokta Chris Ngige zai jagoranci zaman sulhu tsakanin Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Kungiyar Kwadago ta Najeriya.”
Hakan na zuwa ne bayan sa-toka-sa-katsi tsakanin ’yan kwadago da El-Rufai wanda ya ce sallamar ta zama tilas, saboda kudaden albashi ke cinye sama da kashi 80 na kudaden da Jihar take samowa daga Gwamnatin Tarayya.
A ranar Laraba, El-Rufai ya yi barazanar sanya kafar wando da Shugaban NLC, Ayuba Wabba da sauran shugabannin kwadago har sai zuwa Jihar Kaduna ya gagare su.
Gwamnan ya ce zai tabbata an daure shugabannin kwadagon na tsawon shekara 21, bayan tun da farko ya sanar da neman su ruwa a jallo kan zargin gurgunta tattalin arziki da lalata kayan gwamnati.
A ranar Larabar ya sanar da korar daukacin ma’aikatan jinya da ke kasa da mataki na 14 saboda shigarsu yajin aikin, ya kuma ba da umarnin a dauki sabbi da za su maye gurbinsu.
Ya kuma yi barazanar korar ma’aikatan Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da ba su je wurin aiki ba a lokacin yajin aikin.