Dambarwar da ke tsakanin Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki sabon salo inda NLC ta sanar da neman Gwamna Nasir El-Rufai ruwa a jallo.
Kungiyar kwadagon ta kuma ce za ta shiga yajin aiki a fadin Najeriya daga ranar Litinin, saboda yadda aka dauko hayar ’yan daban domin su tarwatsa zanga-zangar lumanar da suke gudanarwa.
- Halima Djimrao za ta jagoranci gabatar da shirin ‘Daga Laraba’
- Gwamnatin Tarayya ta shiga rikicin ’yan kwadago da El-Rufai
“Muna kira ga jama’a da kuma jami’an tsaro su ba mu rahoto a duk inda suka ga El-Rufa’i, mun bukaci jami’an tsaro su kamo shi ya fuskanci hukunci kan sallamar da ya yi wa ma’aikata ba bisa ka’ida ba” inji kakakin NLC na Kasa Kwamared Nasir Kabir, a hirarsa da Sahen Hausa na BBC.
NLC ta kuma yi alkawarin tukwici mai tsoga ga wanda ya kamo El-Rufai, wanda ta bukaci jami’an tsaro su tsare shi domin ya fuskanci hukunci kan sallamar dubban ma’aikata ta haramtacciyar hanya.
Matakin na ’yan kwadago martani ne ga El-Rufai wanda a safiyar Talata ya yi alkawarin tukwici mai gwabi ga duk wanda ya kawo masa Shugaban NLC na Kasa, Ayuba Wabba da sauran jagororin kungiyar.
El-Rufai ya ce yana neman shugabannin na NLC ruwa a jallo ne domin su fuskanci hukunci kan zargin yi wa tattalin arzikin Jihar Kaduna zagon kasa da lalata kadarorin gwamanti da wasu laifuka.
Wabba da El-Rufai sun yi gaba da gaba
’Yan sa’o’i bayan sanarwar ta El-Rufai, Wabba da sauran jagororin NLC sun ci gaba gudanar da zanga-zangar lumana a Jihar, yana mai kalubalantar gwamnan ya zo ya kama shi idan zai iya.
Wabba da ’yan kwadagon da ke tattaki sun yi gaba-da-gaba da ayayin motocin El-Rufai, tsakaninsu bai fi tazarar mita 100 ba, amma gwamnan bai sa a kamo su ba.
Daga baya ’yan daba sun kai wa masu zanga-zangar farmaki a kusa da inda suka hadu da gwamnan, amma masu zanga-zangar suka yi nasarar fatattakarsu.
Kwamaret Nasir ya ce sun gudanar da zaman gaggawa kan
El-Rufai ya sallami ma’aikatan jinya
A yammacin Talata, El-Rufai ya sanar da sallamar daukacin ma’aikatan jinya ’yan matakin aiki kasa da 14 a fadin jihar.
El-Rufai ya kuma umarci daukacin ma’aikatun jihar da su gabatar da rajistar halartar aikin ma’aikata, yana mai cewa duk ma’aikacin Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da bai je aiki ba, to an kore shi.