Kungiyar Kasashen Musulmai ta Duniya (OIC) a ranar Laraba ta yi alla-wadai da hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a Zirin Gaza.
OIC ta kuma soki lamirin kasashen da suke goyon isra’ilar a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Joe Biden yake ziyara a kasar.
- ’Yan sanda sun kama mijin matar auren da aka kashe a Borno
- Bidiyon batsa: Ministan Tsaro da Sakataren Gwamnatin Chadi sun ajiye aiki
Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala taron Ministocin Harkokin Wajen Kasashe mambobinta ta kuma zargi Isra’ila da kai hari a kan asibitin Al-Ahli a ranar Talata, inda ta kashe sama da mutum 471 a Zirin na Gaza.
Kasashen Larabawa ma a daidaikunsu sun yi alla-wadai da harin na Isra’ila wanda ya yamutsa hazo a yankin Gabas ta Tsakiya.
To sai dai a yayin da yake ganawa da Firaminin Isra’ila, Benjamin Netanyahu a ranar Laraba, Shugaba Biden ya bayyana goyon bayan kasar shi ga Isra’ila cewa wani makamin roka da ’yan ta’adda suka jefa ne ya yi kuskure ya fada kan asibitin.
Bugu da kari, kungiyar ta OIC ta kuma soki lamirin Majalisar dinkin Duniya saboda ta ki tsawatarwa a daina yakin. (AFP)