✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama mijin matar auren da aka kashe a Borno

’Yan sanda sun kama mijin matar auren da aka kashe a Borno

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta kama mijin marigayiya Fatima Alhaji Bukar da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kashe ta a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A ranar Talata ce wasu da ba a kai ga gano su ba ne suka kashe Fatima a gidanta da ke Dikechiri Bayan Gidan Dambe a Maiduguri.

Rahotanni sun ce wadanda suka kashe matar sun daure ta da igiya, inda suka rufe bakinta don gudun kada ta yi musu ihu tare da daba mata wuka a sassa daban-daban na jikinta, wanda a karshe ya yi sanadin mutuwarta.

Wata majiya a cikin iyalan ta ce an kama mijin matar mai suna Adam Alhaji Ibrahim ne a ranar talata da daddare, bayan Gwamna Babagana Umara Zulum ya umarci hukumomi da su mayar da gawarta zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin a fadada bincike.

A baya dai kafin umarnin Gwamnan, iyalan ta sun sanya ranar Laraba da karfe 2:00 na rana domin yi mata jana’iza a gidanta da ke Maiduguri.

Gwamnan ya bayar da umarnin a bincika tare da bankado aika-aikar tare da gurfanar da su gaban kuliya.