Wata kungiya mai fafutikar samar da zaman lafiya a Jihar Kano da ake kira da `Kano Peace Debelopment Initiatibe (KAPEDI)` ta yi kira ga dukan jam’iyyun da ’yan takarar da ba su gamsu da sakamakon zaben da ya gudana ba, su bi hanyoyin da shari’a da kundin tsarin mulki suka tanada wajen bin hakkokinsu.
Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin takardar da Darakta Janar kuma Sakatarenta, Garba Aliyu Gezawa ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Kano.
Kungiyar ta tunatar da ’yan takarar game da yarjejeniyar zaman lafiya da suka sanya hannu a kai wacce ta dora amana da hakkin ganin an samu zaman lafiya kafin da lokaci da kuma bayan zabe.
Kungiyar KAPEDI ta ja hankalin matasa a kan muhimmancin zaman lafiya, inda ta yi kira gare su da kada su yarda a ingiza su su aikata ayyukan assha da tayar da hankali da za su jawo salwantar da rayuka ko dukiya. “Mun kula cewa ta bijirewa yin barna daga matasa ne kawai za mu samu zaman lafiya da zai taimaka wajen ciyar da jiharmu gaba,” inji kungiyar.
Sai ta jinjina wa jami’an tsaro musamman ’yan sanda kan jajircewar da suka yi wajen ganin an gudunar da aikin zabe lafiya tare da yin kira gare su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu ta bin hanyoyin da suka kamata ba tare da sanya son zuciya a ciki ba.