Kungiyar Kanikawa ta Kasa reshen Jihar Kebbi ta zabi sababbin shugabannin da za su ja akalar kungiyar.
An gudanar da zaben shugabannin ne a dakin taro na makarantar Aikin Jinya da Ungozoma da ke Birnin Kebbi, inda shugabannin kungiyar suka koma kan kujerunsu ba hamayya.
Muhammadu Sani ne Shugaba, sai Actor Baba Jede Mataimakin Shugaba, sai Tiphs Olawale a matsayin Sakatare, sai Ma’aruf Abdulganiyyu, Ma’aji sai Francis Marchel Mai binciken Kudi sai Bamaiyi Mamud Sakataren Hulda da Jama’a sai Ibrahim Momoh Sakataren Tsare-Tsare da kuma Sama’ila Haruna Sakataren Kudi. Sauran sun hada da Abdullahi Adamu Mataimakin Jami’in Hulda da Jama’a da Bilyaminu Umar Mataimakin Sakatare da Ezerik Okope a matsayin Mashal da Mohammodu Bamaiyi a matsayin Amintacce na Daya.
Da yake jawabi bayan kammala zaben, Alhaji Abubakar Nasiru Mataimakin sSugaba na yankin Arewa maso Yamma na kungiyar ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben lafiya.
Ya ce wannan zabe da suka gudanar ya zo musu da sauki sosai, domin an samu sulhu a tsakanin ’yan takara.
Ya ce ba abin da ya kara saka shi farin ciki kamar yadda ’yan kungiyar suka hada kansu suka zabi kabilu daban-daban da za su jagorance su.
Ya yi kira ga sabon shugaban da ya rike wannan amana da adalci musamman ganin yadda ’ya’yan kungiyar suka taru suka zabe shi a matsayin shugaba ba hamayya.
Da yake nasa jawabi a wajen taron Manajan Kamfanin Ammasco na Jihar Kebbi Alhaji Bilya Hamza Idris, ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su rike wannan sana’a da daraja domin sana’a ce mai matukar muhimmanci a duniya.
A jawabin zababben shugaban Muhammadu Sani, ya bayyana cewa ya yi matukar farin ciki da wannan zabe da aka yi masa, sannan ya bayar da tabbacin cewa zai yi kokari wajen ganin an bi dokoki da tsarin wannan kungiya. Sannan ya ce asalin manufar kafa wannan kungiya ita ce domin kanikawa su taimaki junansu, don haka ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen ganin sun taimaki junansu.