kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta bullo da wani shiri na taimaka wa marayu da marasa galihu a al’umma. A yanzu haka, kungiyar tana da fiye da marayu dubu 36 a duk fadin kasar nan, wadanda ke cin moriyar shirin. Shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayar da karin haske a hirarsa da wakilinmu da yadda jama’a za su ci moriyar:
Aminiya: Akaramukallah, mene ne makasudin bullo da wannan shirin?
Sheikh Bala Lau: Muna da wannan shirin mai suna a Turance ‘Families In Difficult Circumstances Support Scheme’, wato shiri ne da muka bullo da shi ta yadda za mu taimaka wa mutane masu rauni da marasa galihu da marayu da dangoginsu. Mun lura ne da ayoyin Alkur’ani Mai Girma, bayan wa’azin da Manzon Allah [S.A.W] ya yi wa duniya. Ya fitar da duniya daga duhu zuwa haske, ya kasance jama’a sun shigo addinin Musulunci, saboda addini ne na Allah, wanda yake nuna tausayi da koyar da shi. Annabi ya tausaya wa al’umma matuka. An saukar da Surah, wadda manyan darussanta suka karkata wurin tausaya wa masu rauni wato Suratul Nisa’i. Galibi duk inda ka ga masifa ta auku ko ta fada wa al’umma, mata ne suka fi wahala. Su ke kula da yara kanana, su mazajen da suka rasu suke yawan bari da makamatansu. Alkur’ani, har ila yau, ya koya mana yadda za mu tausaya wa marayu, tare da tsoron Allah. Annabi, har ila yau, ya nuna duk wanda ya taimaka wa maraya, zai yi makwabtaka da shi a Aljannah, haka kuma wanda ya taimaka wa mata wadanda mazansu suka rasu suka bari. Lura da wadannan ayoyin da hadisai ne suka sa muka kafa wani kwamiti, wanda muka kirkiro wata kungiyar da za ta bullo da hanyoyin da za mu tallafa wa wadannan mutanen bisa yadda aka tsara, bayan wa’azin da muke gudanarwa, wanda wannan da Da’awah su ne manyan manufofinmu.
Akwai mutanen da suke kwance a asibiti suna bukatar taimako. Wasu wadanda ba musulmi ba, sun riki wannan akidar, me zai hana mu gudanar da shi tunda babban aikinmu ne kuma mu muka fi cancantar aiwatar da su don wasu jama’a su yi koyi da mu? Nan ba da dadewa ba, za mu gudanar da tsare-tsaren cigaba da inganta shirin fiye da yadda yake a halin yanzu. A lissafin da muka yi cikin watan Ramadan na bara, akalla kowace jiha ba ta rasa mutane dubu daya zuwa dubu biyar da aka kebe su marayu ne zalla, musamman a jihohin da ke shiyyar Arewacin Najeriya, wadanda ke cin moriyar shirin.
Akwai jihohi wadanda suka zabo yara kanana, wadanda ba su wuce shekara 10 ba, suka dauki bayanansu kuma suka sa su a makarantu don neman ilimin addini da na zamani, daga firamare zuwa jami’a da izinin Allah. Wannan ya hada da kayan makaranta da kudin makarantar da yadda za mu kula da su. An kawo mini jerin sunayen irin wadannan yaran na Jihar Adamawa. Jihar Kano ma haka lamarin yake. A Jihar Katsina akwai wani Bawan Allah, ga gwamnatin jihar ta taimaka an yi gagarumin taro, wanda aka ba wasu daga cikin iyayen wadannan marayun kekunan dinki, wasu kuma babura, wadansu ma har motoci suka samu duka karkashin wannan tsarin da Shugaban kungiyar na Jihar Katsina da Ambasada Garba Aminchi suka tabbatar. Sun kokarta sun samo gudunmuwar babura tirela biyu daga gwamnatin jihar. Har ila yau akwai wani bawan Allah, wanda shi kadai ya samar da tirelolin babura da motoci, duk don mabukata su ci moriya. Ban da wannan mun bullo da wani tsarin taimaka wa mutanen da ke da lalurar makanta da ta yanar ido. A Jihar Katsina aka cire wa irin wadannan mutanen yana ,wanda wani mutum da ake kira Alhaji Barau Mangal, mai kamfanin Mad Air, ya taimaka matuka. Wannan ya sa a duk wata uku, muna yi wa mutanen da ba su kasa 300 wannan aikin da magunguna saboda Allah.
A bana mun kira ’yan kasuwa, a taron wayar wa juna kai game da muhimman al’amura yadda jama’a za su samu sauki a Ramadan, yayin da farashin kayan masarufi kan tashi. Mun gayyaci manyan ’yan kasuwa aka tattauna. Muna da burin cigaba da gudanar da irin wadannan tsare-tsare don kara kwadaita wa jama’a da dama su rungumi irin wannan akidar yadda sauran kasashen musulmi ke yi.
Aminiya: Wace hanya kuke bi domin tantance ainihin marayu daga dandazon jama’ar da ke kwadayin cin wannan moriyar?
Sheikh Bala Lau: Kowace jiha tana da kwamitin da ke kula da wannan al’amari. Muna da rahoton kowace jiha a wannan ofishin. Abin da ake yi shi ne ana daukar sunan maraya da shekarunsa da lambar gidansu, wato adireshi ke nan. Haka kuma lambar wayar wanda ke kula da shi. Mun yi haka ne domin shaida wa jama’a cewa wannan shirin da gaske muke. Idan kana bukata, sai ka zabi lamba, ka buga kuma ka bincika. Ana tara su ne a masallatan unguwanni inda ake wannan tantancewa domin gano marayun da iyayensu maza suka rasu kuma ba su balaga ba; ban da wadanda iyayensu mata suka rasu. Bayan an kammala ne ake zartar da shawarar irin tallafin da suka cancanta daga kayan abinci zuwa tufafi da tallafin karatu. Mun tsara shirin ne ta yadda jama’a za su samu abin da ya sawwaka daga kungiya kashi-kashi. Wannan ya sa muke koya musu sana’o’in da za su samu abin dogaro a rayuwa, su ma su taimaka wa wasu. Muna fatan samar da Cibiyar Koyar da Sana’o’I, gwargwadon hali.
Aminiya: Wane tanadi kuka yi domin dorewar shirin?
Sheikh Bala Lau: Muna da wani tsari na ‘MANARA’. Tsari ne da ’yan kungiya za su tallafa gwargwadon abin da ya sawwaka duk Juma’a. Ga duk wanda yake neman karin haske game da wannan shirin, yana iya ziyartar kowane daga cikin masallatanmu. Misali muna da masallatai dubu daya na Juma’a, sannan ka kaddara a kowane masallaci muna da ’yan kungiya dubu daya wadanda ke bayar da gudunmuwa. Ka ga ke nan, a duk mako muna da mutum miliyan daya, wadanda ke tallafa wa shirin, babu matsala. Ka ga babu abin da za mu ce, sai godiya ga Allah. Mun samu hanyar da jama’a za su cigaba da tallafa wa wannan shirin. Babbar fargabarmu ita ce kada al’amarin ya fuskanci kowane irin nau’i na matsala. Yanzu haka, mun zakulo mutanen da muke gani amintattu ne muka sa su a kwamitin da za su yi aikin kokarin da muka sa a gaba na kafa jami’a domin kara azamar da muke ita na bayar da gudunmuwa ga wannan fanni na ilimi da muka dade muna yi.
Aminiya: A karshe, mece ce fatarka?
Sheikh Bala Lau: Babbar fatata ita ce Allah Ya dawo da zaman lafiya a wannan kasa tamu. Magana ta gaskiya, wannan kasar tana bukatar addu’armu baki daya. Ina kira ga shuagabannin wannan kasa a matakin tarayya da jihohi da su shirya wani taro na musamman domin samar da hanyoyin da za a shawo kan matsalolin da suka addabe mu. Bayan haka, kowa ya canza halayensa daga marasa kyau zuwa wadanda jama’a za su yi koyi da su. Allah Ya kyauta.