✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar JESA ta shirya muhawara kan yaki da cin hanci

Kungiyar Dalibai ’Yan Asalin Masarautar Jama’a (Jama’a Emirate Students Association – JESA) ta shirya gasar muhawara karo na farko a tsakanin ’ya’yanta da ke karatu…

Kungiyar Dalibai ’Yan Asalin Masarautar Jama’a (Jama’a Emirate Students Association – JESA) ta shirya gasar muhawara karo na farko a tsakanin ’ya’yanta da ke karatu a manyan makarantun kasar nan.

Gasar, wanda aka gudanar a dakin taro na Women Multipurpose Hall da ke garin Kafanchan, ya samu wakilcin dalibai daga makarantu shida na makarantu 10 da aka sa ran halartarsu inda aka tafka muhawara kan shirin fallasa masu almundahana da dukiyar kasa da wannan gwamnati ta fito da shi, shin da gaske take ko kuwa akwai lauje cikin nadi?

An tafka muhawara mai zafi, inda a karshe daliban masarautar Jama’a da ke karatu a Jami’ar Bayero ta Kano suka zamo zakaru.

Daliban Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi ne suka zo na biyu yayin da daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya suka zo na uku.

Da yake yi wa Aminiya karin haske kan makasudin shirya muhawarar, Shugaban Kungiyar, Akilu Ibrahim Musa, kyankyasar BUK, ya ce sun yi tunanin kirkiro da wannan muhawara ce a tsakanin daliban Masarautar Jama’a da ke karatu a manyan makarantun kasar nan a kokarinsu na gwada irin hazakar da suke da shi tare da musayar fahimta da karin gogewa da wayewa kan abubuwan da ke wakana a cikin kasa da waje da makaranta.

“Mun zabi wannan maudu’in ne don kara zaburar da junanmu da kuma bayar da irin tamu gudunmawar wajen yaki da cin hanci da rashawa. Da yawan mutanenmu ba su san ta yadda za su fallasa masu almundahana ba yayin da wadansu kuma ke tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo idan suka fallasa masu laifin. Sannan ta bangaren gwamnati wane tabbacin kariya za ta bayar baya ga ladar da za a ba wanda ya yi fallasar idan masu laifin da ya fallasa suka samu gata?”

Makarantun da suka shiga gasar sun hada da Jami’ar Al-Kalam ke Katsina da Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya-Kafanchan (KSCOE) da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya (FCE).

Sauran da aka gayyata ba su samu halarta ba sun hada da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), Bauchi da Kwalejin Kiwon Lafiya da Ungozoma ta Jihar Kaduna da ke Kafanchan (KSCON&M) da Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).