✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Hisburrahman ta bukaci Buhari ya duba almajirai

kungiyar Makarantun Allo ta Jihar Kano wacce aka fisa ni da Hisburrahman Fitilawatil kur’ani ta yi kira ga zababen Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya…

kungiyar Makarantun Allo ta Jihar Kano wacce aka fisa ni da Hisburrahman Fitilawatil kur’ani ta yi kira ga zababen Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba halin da almjiran kasar nan ke ciki ya kuma lalubo musu hanya don inganta rayuwarsu.

Wannan kira ya fito daga Shugaban kungiyar Alaramma Tukur Ladan a lokacin da yake tatuanawa da jaridar Aminiya a Kano. Alaramma Tukur ya bayyana cewa an dauki tsawon lokaci gwamnatocin da suka gabata na yin alkawurra da dama game da kyautata rayuwar almajirai a kasar nan, sai dai har yanzu ba a samu gwamnatin da ta tsaya ta cika irin wadanann alkawurra ba. “An dade ana yi mana alkawurra don inganta rayuwar almajirai masu karatun allo, amma sai dai cika alkawarin ya gagara. Ko gwamantin mai barin gado ta yi alkawarin gina tsangayoyin allo guda dari a kowacce jiha da ke yankin Arewacin kasar nan, sai dai tun da aka gina guda daya tak a Jihar Sakkwato ba a sake kara maganar ba,” inji shi.
Alaramman ya bayyana ire-iren abubuwan da almajiran ke bukata, inda ya ce suna bukatar wurin da za su rika tsugunar da almajiransu. A cewar Alaramam suna bukatar jarin da za su koya wa almajiransu ayyukan sana’ar hannu don dogaro da kansu. Ya ce: “Baya ga matsugunni da muke bukata don saukar alamjiranmu kuma muna so gwamnati ta fito da wani tsari, inda za a rika tallafa mana da jari ko kuma gwamnati ta dauki almajiranmu ta koya musu sana’o’i don dagaro da kansu. Wannan shi zai kawo karshen bara da ake kukan almajirai na yi,” inji shi.
Alaramma ya kara da cewa, “Muna da kyakkyawan zato ga wannan gwamnati ganin cewa gwamnati ce ta jama’a, don haka muke kira ga gwamnati tun daga sama har kasa da ta taimaka mana ta duba almajirai.”
Har ila yau, shugaban kungiyar ya yi kira ga jama’a da su dukufa wajen addu’o’i akan Allah Ya taimaki kasar nan ya kuma bayar da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.