✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Haske ta koka kan yadda Yarabawan Legas ke bata musu suna

kungiyar taimakon juna, wacce ake kira Haske Association da ke unguwar Faba a yankin Agege, Jihar Legas, ta bayyana alhininta kan yadda kabilun Yarabawan Legas…

Wasu daga cikin shugabanni da membobin kungiyar Haske Association.kungiyar taimakon juna, wacce ake kira Haske Association da ke unguwar Faba a yankin Agege, Jihar Legas, ta bayyana alhininta kan yadda kabilun Yarabawan Legas suke bata wa ’ya’yanta suna  ta hanyar kiran su da ’yan boko haram.
Shugaban kungiyar, Malam Iliyasu Idris shi ne ya yi furucin haka, yayin da yake ganawa da Aminiya a makon jiya, inda ya yi nunin wai da zarar wani sabani ya shiga tsakanin wani Bahaushe da Bayarabe sai ya ce masa dan boko haram. “Gaskiya babbar matsala ce yadda kabilun Yarabawa suke ci mana mutunci ta hanyar bata mana suna. Da zarar wani  sabani ya shiga tsakaninsu da Bahaushe, sai ka ji ya ce masa dan boko haram. Hakika muna bakin cikin yadda wannan al’amari yake faruwa. Saboda haka muna kira ga al’ummar Yarabawa su daina irin wadannan kalamai domin mu neman arziki muka zo Legas, ba tashin hankali ba. Kuma kowa ya san Bahaushe ba dan ta’adda ba ne kuma ba mai ta da zaune tsaye ba ne”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Wani abu da yake bata mana rai shi ne yanzu a yankin Kudu idan dai mutum Bahaushe ne su kawai daukarsa suke yi dan boko haram ne. Akwai wani yaro dan acaba da wani sabani ya shiga tsakaninsa da wani Bayarabe, ana cikin sasantawa sai wani dan uwansa ya ce bai kamata ya yafe mana ba, kamata ya yi ya karbi kudi masu yawa a wurinmu saboda dukkanmu ’yan boko haram ne”.
Da yake karin bayani, sakataren kungiyar, Malam Murtala Uba ya bayyana cewa kungiyar ta tashi tsayin daka don ganin ta kwato ’yancin ’ya’yanta, wadanda suka hada da masu sana’ar acaba da sayar da kayan gwari da masu sayar da kujeru da masu sayar da waya da sauran masu sana’o’i daban-daban.
Murtala Uba ya ce kungiyar ta samu nasarori da suka hada da ba da tallafi ga wanda aka yi wa haihuwa da masu aure da marasa lafiya da sauran lalurori na rayuwa.
Shi ma alkalin kungiyar, Malam Umar Isa ya bayyana cewa kungiyar na kokari wajen cusa da’a da bin doka da oda ga ’ya’yanta, wadanda kuma suka sami fahimtar juna, sakamakon kyawawan manufofin shugabannin kungiyar.