✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar EU ta dakatar da horar da sojoji a Mali

EU ta ce duk da takaicin da ta ji kan ficewar gwamnatin sojin Mali daga kungiyar G5 Sahel, ba za su dakatar da aikin horon…

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta ce za ta dakatar da horon da take bai wa sojoji na wucin gadi a kasar Mali. 

Babban jami’in harkokin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai (EU), Josep Borrell, shi ne ya sanar da haka bayan ganawarsa da ministocin tsaron kungiyar a Brussels babban birnin kasar Beljiyam.

Sai dai Mista Borrell ya ce duk da takaicin da suka ji da matakin gwamnatin sojin kasar Mali da tauka na ficewa daga kungiyar G5 Sahel, ba za su dakatar da aikin horon ba kwata-kwata ba.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai kasar Mali ta sanar da aniyarta ta ficewa daga kungiyar G5 Sahel da kuma rundunar kawancen yaki da ta’addanci a Yammacin Afirka da ke samun tallafin kasashen na Turai.

Babban jami’in na kungiyar EU, ya kalubalanci matakin gwamnatin sojoin Mali ci gaba da aiki da sojojin haya na kamfanin Wagner daga kasar Rasha, wadanda ake zargin su da take hakkin bil Adama.

A shekarar 2017 ne dai aka kafa kungiyar G5 Sahel mai kunshe ne da dakarun kasahen Nijar da Chadi da Burkina Faso da kuma Mauritania da nufin yaki da mayaka masu ikrarin jihadi a yankin Sahel.