✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Danga ta kama masu satar wayoyin lantarki a yankin Toro

Ya’yan kungiyar tsaro da ta Danga a Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi, sun kama wadansu mutane biyu da ake zargi da satar wayoyin…

Ya’yan kungiyar tsaro da ta Danga a Karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi, sun kama wadansu mutane biyu da ake zargi da satar wayoyin lantarki a babban layin lantarki da ke hanyar Bauchi zuwa Jos, a yankin Toro a karshen makon jiya.

Da yake gabatar wa wakilin Aminiya mutanen  a ofishin kungiyar da ke garin Magama Gumau, Shugaban Kungiyar Danga na Karamar Hukumar Toro Alhaji Yusuf Abdullahi ya ce, sakamakon iskar da aka yi   kwanakin baya, turakunan wutar lantarki da suka fito daga Bauchi zuwa yankin sun fadi a kasa, don haka barayi suka rika zuwa suna yanke wayoyin.

Ya ce ganin haka ya sanya suka sanya ido har Allah Ya taimake su, suka kama wadannan mutum biyu; Bashir Dauda da Usman Muhammad.

Ya ce shi da yaronsa suka kama wadannan mutane, lokacin da suke shirin zuwa su yanke wayoyin, kamar yadda suka saba.

Ya ce sun shaida musu cewa kwanakin baya sun zo sun saci wayoyin lantarki a wannan yanki kuma sun je sun sayar a garin Jos, shi ne kuma suka sake dawowa.

Ya ce za su mika mutanen da ake zargi ga jami’an tsaro na farin kaya wato Cibil Defence.

Da yake zantawa da Aminiya daya daga cikin wadanda ake zargin, Bashar Dauda ya yi bayanin cewa shi mazaunin cikin garin Jos ne.

Ya ce jarrabawar karayar arziki ce ta sa ya shiga wannan harka. Kuma ya zo aikin hakar  ma’adani ne a yankin. Sai suka hadu da Usman Muhammad wanda dama unguwarsu daya a garin Jos.

Ya ce shi ne suka yi shawara kan su je su cire wayoyin lantarkin da suka fadi a wajen da ake hakar ma’adanai su kai garin Jos su sayar.

“Muka sanya rana muka samu wani mai mota muka je muka yanke wayar  muka dauka, muka kai cikin garin Jos, muka sayar Naira dubu 33 muka raba kudin.Shi ne muka sake dawowa sai abin bai yiwu ba. Sai muka sake shiryawa ranar Asabar muka dawo muka tsaya cikin garin Magana Gumau, muna shirin ajiye buhun da za mu sanya wayar, da abin yanka wayar.  Shi ne wadannan ’yan Danga suka gani, suka kama mu,’’ inji shi.

Ya ce gaskiya ya yi nadamar wannan abu da suka yi. Ya ce da ya san haka zai faru da ya kara hakuri, kan halin da yake ciki, har Allah Ya ba shi mafita.

Shi ma a zantawarsa da Aminiya, Usman Muhammad ya ce Bashir Dauda ya gaya masa halin da yake ciki. Ya ce masa yaya yake ganin kan wayoyin wutar lantarki nan da suka zube a kasa a wajen da ake hakar ma’adanan nan.

Ya ce suka hadu da wani abokinsa mai suna Anas suka je suka ciro wayar suka kai Jos suka sayar a kwanakin baya. Ya ce shi ne a ranar Asabar abokin nasa ya kira shi a waya kan cewa ya zo. Da ya zo ya  same shi,  sai ya ce masa ya zo ne su je su sake ciro wayar.

“Sai na ce ba zan yi ba,  na daina wancan ma da muka yi,  ina rokon Allah Ya yafe mIni. Sai ya ce mIni shi ke nan bari ya koma gida. Ya juya yanayin kwana sai muka ga dan Danga ya zo ya kama shi, da buhun da ya ajiye a wajen. Sai na yi musu bayani cewa gaskiyar magana wannan buhu da wannan abin yanke waya, ya zo da shi ne domin a je a sato waya. Shi ne suka kawo shi ofishinsu,” inji shi.

Usman Muhammad ya yi bayanin cewa shi dai an yi sata ta farko da shi, da aka sake dawowa aka ce a yi ta biyu ya ce ba zai yi ba. Kuma ya yi nadamar yadda ya kasance a cikin sata ta farko.