✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar CSACEFA ta yunkuro don yakar cin zarafin yara a makarantu

Kungiyar da ke rajin tabbatar da ’yan Najeriya sun sami limi mai inganci ta (CSACEFA) ta yi kira ga daukacin kungiyoyi masu zaman kansu su…

Kungiyar da ke rajin tabbatar da ’yan Najeriya sun sami limi mai inganci ta (CSACEFA) ta yi kira ga daukacin kungiyoyi masu zaman kansu su yaki dabi’ar nan ta cin zarafin yara a makarantun kasa baki daya.
Mai Baiwa Kungiyar Shawara ta Kasa Kan Dokoki da Tsare-tsare, Chioma Osuji ce ta yi kiran yayin da take tattaunawa ta musamman da Aminiya a Abuja jiya.
“Ya zama wajibi ga kungiyoyi masu zaman kansu su hada karfi da karfe su yaki wannan dabi’ar ta cin zarafin yara ta hanyar yin lalata da su ko sanya su a kungiyoyin asiri”. Inji ta.
Ta bayyana cewa masu muguwar dabi’ar cin zarafin yara na cin karensu babu babbaka a sassa da dama na kasar nan.
Saboda haka sai ta shawarci iyaye su sanya ido tare da kula da dabia’ar yaransu don kare su daga muguwar dabi’ar.
Ta ce da zarar iyaye sun ga wata alama ta wani yayi lalata da yaransu ko kuma wani ya sanya su a kungiyar asiri to su gaggauta kai rahotonsa wurin hukuma.
Ta bayyana cewa idan iyaye da malaman makaranta sun yin shiru tare da boye mummunar dabi’ar da suka gano a tare da yara to babu shakka lamarin zai yi illa ga al’umma.
Osuji wacce ta nuna damuwa dangane da samun karuwar cin zarfin yara da garkuwa da jama’a da sauran laifuka a sassa da dama na kasar ta yi kiran a tashi tsaye wajen kawo karshen matsalolin.
Ta ce hada karfi da karfe wajen yakar muguwar dabi’ar hanya ce da za taimaka kwarai da gaske wajen kawo karshen laifuka a tsakanin al’umma.
Ta bayyana cewa kungiyar CSACEFA na da shirye-shirye masu yawa za ta bullo da su nan gaba kadan don tabbatar da cimma burin da ta sanya a gabata na ganin an samar da ilimi mai inganci ga kowa da kowa.
Ta bayyana cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban al’umma wajen kawo bunkasar tattalin arziki da zaman lafiya a kasa baki daya.