Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU) ta tsunduma yajin aiki kai tsaye domin jan kunnen Gwamnatin Tarayya wajen ganin ta cimma yarjejeniyar da suka kulla tsawon shekaru.
Shugaban Kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa na kungiyar a safiyar Litinin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Wayar Hannu Ta Zamo Jinin Jikin Mutane A Yau
- Rasha za ta dandana kudarta muddin ta mamaye Ukraine – Amurka
Aminiya ta ruwaito cewa bayan dogon zaman da kungiyar malaman ta yi cikin daren Litinin, Majalisar Zartaswar ASUU ta amince malamai su fada yajin aikin na tsawon makon hudu kacal domin ganin gwamnatin tarayya ta waiwayi bukatunsu.
Wata majiya a zaman tattaunawar da Majalisar Zartawar ta gudanar, ta ce ASUU ta yanke wannan shawara ce don bai wa Gwamnatin Tarayya damar yin abin da ya kamata ko kuma su tafi yajin aikin sai baba ta gani.
A cewar majiyar, “muna son bai wa gwamnati dama ce don ta yi abin da ya dace domin hana yajin aikin sai baba ta gani.
“Mu ma fa iyaye ne kuma ’ya’yanmu na karatu a jami’o’in amma ba za mu zuba ido harkar ilimi ta lalace a kasar nan ba.
“Muna wannan gwagwarmaya ne domin amfanin kowa, dukkanmu za mu ji dadi ida aka gyara. Manyan masu fada a ji sun sanya baki amma da alamu gwamnati bata shirya ba.”
Tun kafin yanzu ne dai kungiyar ta lashi takobin shiga yajin aiki kan abin da ta kira halin ko-in-kula daga bangaren Gwamnatin Tarayya, inda a watanni baya bayan nan ta rika barazanar shiga yajin aiki amma wadda ake yi don ita ta yi buris.
Yajin Aiki na baya bayan nan da kungiyar ta shiga shi ne wanda ta tsunduma a watan Maris din 2020, biyo bayan rashin jituwa da ta samu da gwamnati kan kudaden da take bai wa jami’o’i da wasu tsare-tsaren albashi da alawus-alawus.
Kungiyar dai ta fara yajin aikin nata ne na watan Maris da nufin matsawa gwamnati ta samar da kayyyakin aiki a jami’o’i domin bai wa dalibai damar koyo da kuma gogayya da takwarorinsu na ko ina a duniya.
Sai dai an janye yajin aikin ne bayan gwamnatin da ASUU sun sanya hannu kan wata yarjejeniya domin biya wa kungiyar bukatunta, abin da ya ba da damar yanje yakin aikin a ranar 24 ga Disamba, 2020.
Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu gwamnatin ba ta gama cika bangarenta ba a yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar malaman jami’ar.
Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin manyan muradan da kungiyar ta ke hankoro akwai neman amincewar gwamnatin a kan tsarin biyan albashin ma’aikatan jami’a da ake kira UTAS sabanin wanda gwamnatin ta bijiro da shi na albashin bai daya da ake yi wa lakabi da IPPIS.