kungiyar masu koyar da harshen Larabci da adabi ta kasa wacce a takaice ake kira (ASALLIN), ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta rika sanya membobin kungiyar a duk wani batu da ya shafi harshen Larabci don su rika bayar da gudunmawarsu.
Shugaban kungiyar na kasa, Dokta M.U Ndagi shi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya ta wayar salula a ranar Litinin din da ta gabata a Abuja.
Ya ce, kamata ya yi duk wani lamari da ya shafi harshen Larabci a rika sanya wadanda suka lakanci harshen.
Ya bayar da misali da hukumar gudanarwa ta makarantar koyar da harshen Larabci da ke garin Gamborin Ngala na Jihar Barno, inda ya ce kamata ya yi wadanda suka lakanci harshen ne suke yin jagoranci.
Ya kara de cewa ya kamata a sanya membobin kungiyar a kwamitin hadaka na ilimi wato (JCCE). Har ila yau, ya ce ya kamata gwamnati ta nada membobin kungiyar a matsayin masu sanya ido a taron kwamitin koli na ilimi na kasa wato (NCE). Hakazalika, ya bayyana rashin jin dadinsa na rashin sanya harshen Larabci a manhajar ilimin kwalejin ’yan sanda da ke garin Wudil a Jihar Kano.
“Dalilinmu shi ne bai kamata a ce wanda ya karanta harshen Turanci ya rika wakiltar wandanda suka karanta na Larabci a wadannan batutuwa ba. Saboda duk wani mataki da za a dauka ya zama mun bayar da ra’ayinmu,” inji shi.
Daga nan sai ya bayyana cewa manufofin kungiyar sun hada da bunkasa tare da goyon bayan duk wani bincike a harshen Larabci da adabinsa.
Ya ce, burin kungiyar shi ne kwadaitar da dalibai karanta harshen Larabci a matakan ilimi da kuma tabbatar da nemo mafita ga kalubalen da ke hana ci gaban harshen Larabci a Najeriya.
Ya bayyana cewa kungiyar tana shirya taruka na kasa shekara-shekara don fadakar da al’umma a kan batutuwa daban-daban.
Saboda haka ya ce shi ya sa kungiyar ta gudanar da babban taronta na 11 a Jami’ar Abuja, inda ta sanya masa taken: Harshen Larabci ba tsaron kasa.
Hakazalika, a cewarsa kungiyar ta gudanar da babban taronta na 10 a Jami’ar Bayero da ke Jihar Kano, inda masana suka tattauna a kan harshen Larabci da Adabi a manyan makarantu a Najeriya.
Ya ci gaba da cewa kungiyar ta zabi maudu’in taronta na Abuja saboda kalubalen tsaro da ke addabar wasu bangarorin kasar nan.