Kungiyar Arewarmu Duniyarmu mai rajin kare hakkin ’yan Arewa mazauna Kudancin kasar ta yi Allah wadai da yadda ake kashe-kashen ’yan yankin a Kudancin Kasar.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rahotanni suka bayyana cewa an halaka wasu mutum biyu da ke sana’ar sayar da nama a Kasuwar Aba da ke Jihar Anambra a Kudu maso Gabashin kasar.
- Abba Kyari ya maka Gwamnatin Tarayya a Kotu kan ci gaba da tsare shi
- APC ta dage babban taronta na kasa har sai abin da hali ya yi
Ya zuwa yanzu dai masu sana’ar dabbobi a garin Aba na ci gaba da neman wasu daga cikin abokanan sana’arsu da suka bata a lokacin wani hari da wasu ’yan bindiga suka kai a kasuwarsu.
A makon da ya gabata ne ’yan bindigar da ake zargin mayakan IPOB ne suka far wa kasuwar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum takwas. Tuni an yi jana’izarsu a cewar rahotanni.
A zantawar da Shugaban Kungiyar Arewarmu Duniyarmu na Kasa ya yi da wakilinmu a Jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Haruna ya yi Allah wadai tare da bayyana rashin jin dadinsa kan yadda aka kashe Fataken shanun da basu ji ba basu gani ba.
Alhaji Ibrahim Haruna wanda kuma shi ne Sarkin Hausawan Tukulma, ya ce yana da kyau gwamnati ta bibiyi wannan al’amari don ganin an biya iyalan wadanda aka kashe diyya sannan kuma ta dauki matakin kare sake faruwar hakan domin kuwa tura ta fara kai ’yan Arewa bango.
Ya kuma ce ba za su ce a dai na kai dabbobi ko kayan abinci Kudancin kasar ba amma dai kungiyar tana kira ga hukumomi da cewa su tashi tsaye don shawo kan irin wannan rikici da a kawone lokaci zai iya rincabewa.
Haka kuma, ya buga misali da kisan da aka yi wa wasu matafiya a garin Jos na Jihar Filato, inda ya nemi gwamnati ta sa baki domin galibi rikicin Jos ya fi shafar mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Alhaji Haruna, ya shawarci ’yan Arewa da su takaita wasu aikace-aikacensu na safarar kayayyakin abinci da Nama da suke kai wa Kudancin Najeriya domin watakila jin zafin an daina kai musu kayan zai sa su dai na kashe mutane.
Ya kuma kirayi manyan Sarakunan Arewa da masu hannu da shuni da Gwamnonin Arewa a kan su zauna da takwarorinsu na Kudi don ganin an shawo kan wannan matsala ta yawan kashe ’yan arewa mazauna Kudu.