✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Ifeanyi Ubah ya riga mu gidan gaskiya

A farkon shekarar nan ce Sanata Ubah ya sauya sheƙa daga jam’iyyar YPP zuwa APC.

Wakilin shiyyar Anambra ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ifeanyi Ubah ya riga mu gidan gaskiya a safiyar wannan Asabar din.

Makusanta sun ce sanatan na jam’iyyar APC ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan a Birtaniya kwana biyu bayan barin Nijeriya.

Sai da ba a fayyace ainihin dalilin mutuwar marigayin ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, amma ana zargin matsalar ciwon ciki ce ta sa ya fita neman lafiya a ƙetare amma ajali ya katse masa hanzari.

A farkon shekarar nan ce Sanata Ubah ya sauya sheƙa daga jam’iyyar YPP zuwa APC , inda ya bayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar Gwamnan Anambra a 2025.

Wasu rahotanni na cewa a bayan nan ya ba da gudunmawar N71m ga jam’iyyar APC a Anambra.

Ana iya tuna cewa, a watan Satumbar 2022 ya tsallake rijiya da baya yayin wani hari da ’yan bindiga suka kai wa ayarin motocinsa a hanyar ta zuwa Nnewi a Jihar Anambra.