Al’ummar Jihar Anambra sun koka kan yadda masu sana’ar POS ke cin karensu babu babbaka inda sukan yi wa jama’a cajin fitar hankali yayin cire sabbin takardun kudi.
Binciken Aminiya ya gano a halin da ake ciki a Jihar, akalla kashi 30 cikin 100 na adadin kudin da aka cire masu POS ke cajin mutane.
- Karancin takardun kudi: Gwamnonin APC 3 sun maka Buhari a kotu
- Matasa na zanga-zangar goyon bayan canjin kudi a Abuja
Alal misa, a Awka, babban birnin jihar, Naira 3,000 masu POS kan karba kan kowace Naira 10,000 da aka cira idan sabbin kudi ne, sannan N2,000 idan tsohuwar Naira za a ba mutum.
A wasu wuraren kuwa, Naira 1,500 sukan karba kan kowace N5,000 da aka cire, sannan N300 a kowace N1,000 in dai da sabuwar takardar kudi ce.
Wasu daga cikin ‘yan jihar da Aminiya ta zanta da su, sun koka kan yadda masu POS ke tsauwala wa jama’a da caji musamman kuma a irin wannan hali da ake ciki.
“Gaskiya na ji zafin yadda na tura a ciro mini N10,000 na ga an caje ni N3,000, hakan na nufin N7,000 ke nan na cira.
“Wannan ba daidai ba ne ko kadan, so ake a kashe talaka.
“Ba mu da man fetur sannan babu kudin da za mu ciyar da iyali, wannan ba keta ba ce?” in ji Joel Mbachi.
Shi kuwa Philip Obasi, cewa ya yi “Ba na tunanin zan juri asarar kudin da na wahala na nema. Gaskiya idan ba a yi wani abu a kan haka ba, talaka za su juya.”