Kungiyar Ansaru Faidatul Tijjaniyya da ke garin Kafanchan ta gudanar da zikirin shekara tare da yi wa kasa addu’a da ta saba gudanarwa a kowace Juma’a ta biyu ta kowane watan Muharram.
An gudanar da taron addu’ar na bana wanda shi ne karo na shida a Babban Masallacin Juma’a da ke Kofar Fadar Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II a garin Kafanchan fadar Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna.
A lokacin da yake yi wa Aminiya karin bayani bayan kammala zikirin da addu’o’in, sabon Shugaban Kungiyar, Alhaji Hussaini Muhammad BabaTahir ya ce ana gudanar da wannan addu’ar ce don nuna godiya ga Allah bisa ga shiga sabuwar shekarar Musulunci ta Hijira ta hanyar gabatar da zikiri da yin addu’o’in zaman lafiya ga Masarautar Jama’a da Karamar Hukumar Jama’a da Jihar Kaduna da kuma kasa baki daya tare da rokon Allah alheran da ke cikin shekarar.
“A wannan karo mun hada da yi wa shugaban kungiyar na farko wanda kuma ya assasa aikin alherin, marigayi Sulaiman Tijjani Tahir da aka sace shi tare da yi masa kisan gilla a cikin watan azumin da ya gabata,” inji shi
Alhaji Husaini M. Tahir ya ce an assasa kungiyar ce don daukar nauyin addu’o’i amma suna gudanar da gyare-gyaren masallatai a ciki da wajen garin Kafanchan.
Da yake yi wa Aminiya karin haske, Shugaban Kungiyar Fityanul Islam reshen Kudancin Kaduna, Sheikh Aminu Kassim Kafanchan ya ce bayan kokarin da ake yi a aikace ta hanyar shirya tarurrukan fadakarwa da sauransu, dole ne kuma a rika komawa ga Allah a dunkule da daidaiku don yin addu’ar samun zaman lafiya da neman mafita ga halin da kasa ta ke ciki.
Sheikh Muhammad Mushry Dahiru Bauchi ne ya jagoranci gabatar da addu’o’i na musamman bayan Sallar Magariba.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron addu’ar har da Babban Limamin Jama’a da Na’ibinsa da Shugaban Fityanul Islam na Kudancin Kaduna da Sheikh Yahaya Nuhu Sallau Kano da Shugaban Kungiyar Malaman Makarantun Allo ta Kudancin Kaduna, sai Babban Mai masaukin baki Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II.
Daruruwan Musulmi ne daga garuruwan Kudancin Jihar Kaduna suka halarci taron zikiri da addu’ar.