✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta tallafa wa ’yan firamare 120 da kayan karatu

Wata kungiya mai zaman kanta a Jihar Gombe da ke kare hakkin yara kanana da samar da ci gaba, mai suna ‘New Age Initiatibe for…

Wata kungiya mai zaman kanta a Jihar Gombe da ke kare hakkin yara kanana da samar da ci gaba, mai suna ‘New Age Initiatibe for Youth Debelopment’, ta tallafa wa ’yan makarantar firamare 120 da yunifom da jakakkunan makaranta da sauran kayan karatu a garin Kumo hedkwatar Karamar Hukumar Akko ta Jihar.

Da yake zantawa da wakilinmu a Gombe, Shugaban Shirye-Shirye na Kungiyar, Malam Yahaya Mohammed  Kumo, ya ce kungiyar tana gudanar da aikace-aikacenta ne a bangarori uku da suka hada da ilimi da kiwon lafiya da ayyukan raya karkara.

Malam Yahaya, ya ce Kungiyar New Age Initiatibes a bangaren ilimi tana kokarin rage yawan matsalolin da suke shafar al’umma da kuma rungumar marayu da marasa galihu.

Ya ce ganin haka ne ya sa suka shirya bikin raba kayayyakin ga yaran makarantun firamare 120 a makarantun garin Liman da Jauroji da kuma firamare ta Tike da suke garin Kumo.

Ya bayyana cewa, kungiyar ta tattara tallafin ne daga mambobinta da kuma tallafin wasu kungiyoyi da daidaikun jama’a.

Shugaban ya kuma ce nan gaba suna shirin fadada shirin zuwa makarantun sakandare a fadin jihar domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Sai ya bayyana cewa kafin wannan tallafi kungiyarsu ta dauki nauyin dalibai 150 da suke karatu a jami’oin kasar nan, inda wadansu suke karatun likita wadansu biyar kuma suke makarantar horar da lauyoyi (Law School).

Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni su hada kai da Kungiyar New Age don fadada shirin da zai amfanar da ’ya’yan marasa galihu da marayu.