✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiya ta raba wa marasa galihu kayan abinci da tufafi a Ajingi

Kungiyar ta saba rabon irin wannan tallafi duk shekara don saukaka wa marasa galihu

Kungiyar ci gaban Unguwar Dugwal (UDDA) da ke Karamar Hukumar Ajingi a Jihar Kano, ta tallafa wa marasa galihu da kayan abinci da tufafi kamar yadda ta saba.

Tallafin dai al’ummar unguwar ne masu hannu da shuni da ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati, ke hada kudi don sayen kayan su raba wa marasa galihu don rage musu radadi a watan azumi.

Ko a makon da ya gabata, sai da kungiyar ta raba wa wasu masallatai da ke unguwar tabarmi da wasu kayayyaki na dubban Nairori.

Da ya ke zanta wa da Aminiya a lokacin rabon kayan tallafin, shugaban kungiyar, Malam Umar Isma’il, cewa ya yi kungiyar ta saba gudanar da irin wannan tallafi duk shekara a unguwar, amma a hankali za su fadada zuwa wasu unguwannin Karamar Hukumar saboda aiki ne na alheri.

Shi ma Magatakardar kungiyar, Alhaji  Abbas Ubale Ajingi, cewa ya yi mambobin kungiyar ne suke hada abin da suke da shi daga albashinsu da ribar da suke samu daga kasuwancinsu sannan suke sayan kayan da ake rabawa.

Abbas Ubale, ya yi amfani da damar ya yi kira ga daidaikun jama’a da masu rike da mukaman gwamnati da su shigo su ba da tasu gudummawar don fadada tallafin zuwa wasu unguwanni.

Bikin rabon kayayyakin ya gudana ne a kofar gidan mai unguwar Dugwal, Alhaji Adamu Sa’adu, wanda ya samu wakilcin Aminu Sa’adu, inda aka raba wa mutum 20 kayan abinci da suka hada da shinkafa da taliya.

Sai kuma yadi na maza da turmin atamfa na mata 12; maza shida mata shida.

A lokacin rabon kayan wani bawan Allah ya bai wa mutum 12 da suka samu yadi da atamfar kudin dinki don shi ma ya shiga cikin ladan, yayin da wani ma ya sake ba da katan hudu na taliya, wasu kuma kudi don tallafa wa wanda ba su samu ba.

Wani mai larurar makanta da ya samu tallafin Malam Muhammad Isa, ya gode wa kungiyar ta UDDA a madadin wadanda suka amfana, inda ya ce duk shekara kungiyar ba ta mantawa da su takan tara su ta ba su irin wannan tallafi.

%d bloggers like this: