Kungiyar Wayar da kai kan Kyakkyawan Shugabanci da Zaman Lafiya da Ci gaba (Awareness for Good Leadership, Peace and Debelopment- AGLPD) ta yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya dawo da ’yan sa-kai na ’yan banga cikin aikin dawo da tsaro a jihar.
Kungiyar ta mika bukatarta ce yayin wata zanga-zangar lumana da ta shirya a harabar Masaukin Gwamnan Jihar da ke Asokoro a Abuja.
A jawabin Shugaban Kungiyar da ya karanta wa ’yan jarida, Malam Abdullahi Aliyu Katsina, ya ce sun gudanar da taron ne don nuna damuwarsu kan matsalar rashin tsaro a jihar; inda ya bukaci gwamnatin jihar ta dage takukunmin da tasa a kan ’yan banga a jihar.
Ya ce: “Hare-haren da ake kaiwa kan kauyuka a Jihar Katsina sun nuna yadda mutanen jihar suke fama da rashin tsaro wata tara bayan an dakatar da ’yan banga a jihar ba tare da kawo wani mataki a madadin haka ba.”
Kungiyar ta soki gwamnatin jihar kan yin biris da wani rahoton taron da tsofaffin janar-janar na soja da dattawa da manyan ’yan sanda da sauran masu fada-a-ji a jihar suka yi, inda suka gabatar da matakan tsaro da za a iya dauka wajen inganta tsaro a jihar.
Ya ce: “Wata tara da suka wuce, an yi taron tsofaffin manyan hafsoshin soja da dattawa da manyan ’yan sanda da sauran masu fada-a-ji a Jihar Katsina; saboda samar da tsaro a jihar: amma Gwamnan bai yi aiki da kudirorin da suka gabatar masa ba.”
Takardar korafin da kungiyar ta gabatar ta bukaci, Gwamnan ya bude kofofinsa saboda sauraron korafe-korafen jama’a da shawarwari domin kawo dawwamamen zaman lafiya a jihar.
Jami’in Hulda da Jama’a na Gwamnan, Alhaji Abdulkadir Karfi ya karbi takardar korafin kungiyar ta hannun wani ma’aikacinsa, Dahiru Shu’aib, inda ya yi alkawarin mika ta ga Gwamnan Jihar.