Wata kungiyar kasa da kasa ta Plan ta kaddamar da wani sabon shirin tara audugar mata a daukacin makarantun Sakandaren mata da ke Jihar Bauchi, domin bukatar gaggawa yayin da suke al’ada.
Jagoran shirin, Mista Afolabi Ahmed ne ya bayyana hakan lokacin da yake mika audugar ga Hukumar Gudanarwar Sakandaren Gwamnati ta Manu da ke Karamar Hukumar Ningi.
- Mun kashe ’yan Boko Haram da ISWAP 31, mun kama 70 —DHQ
- Buhari ya sallami Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta
Ya ce shirin guda ne daga wanda kungiyar ke yi na murnar zagowar ranar Ilimin ’Ya’ya Mata ta Duniya da ake gudanarwa ranar 11 ga Oktoban kowacce shekara.
Afolabi ya ce da audugar da za a tara, za a rage yawan daliban da ke kin zuwa makaranta sakamakon zuwan al’adarsu, har sai bayan sun kammala.
Ya kuma ce shirin ya samu tallafin kungiyar Kotex, kuma za a shafe shekaru biyu ana aiwatar da shi a makarantu 32 na Kananan Hukumomin Ningi da Katagum da Bauchi da ke jihar.
A hannu guda kuma, wakilan Ma’aikatar Harkokin Mata da ta Lafiya, hadi da ta Ilimin jihar, sun jaddada bukatar wayar da kan dalibai maza kan matsalolin da suka shafi al’adar mata, domin kawo karshen kyamar da wasunsu ke nuna wa matan lokacin da al’adar ta zo musu.