Kulob din kwallon kafa na Real Madrid da ke Sifen a ranar Talatar da ta wuce ne ya kafa sabon tarihi a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai watau UEFA Champions League bayan ya lashe wasanni 6 a matakin farko na gasar.
A wasan karshe da kulob din ya yi da kulob din Ludogorets na Bulgariya, Madrid ce ta samu nasara a wasan da ci 4-0.
Tun da farko kulob din ya taba samun irin wannan nasara a kakar wasa ta 2011 zuwa 2012 a gasar, bayan ya lashe wasanninsa shida ba tare da rashin nasara ko yin kunnen doki ba.
Yanzu kulob din ya kafa sabon tarihi a gasar a matsayin wanda ya lashe wasanni 6 har sau biyu ba tare da yin kunnen doki ko rashin nasara ba.
Haka kuma kulob din ya kafa sabon tarihi na lashe wasanni 19 a jere fiye da kowane kulob a Sifen. Da ma kulob din yana kan-kan-kan ne da na FC Barcelona a Sifen a matsayin wadanda suka taba lashe wasanni 18 a jere a dukkan wasanninsu sai ga shi Real ta wuce FC Barcelona bayan ta samu nasarar lashe wasa a karo na 19 ya zuwa ranar Talatar da ta shige.
Kulob din Madrid ya kafa sabon tarihi
Kulob din kwallon kafa na Real Madrid da ke Sifen a ranar Talatar da ta wuce ne ya kafa sabon tarihi a gasar zakarun kulob-kulob…