Daya daga cikin daliban Kwalejin Gandun Daji, da ke Afaka a Jihar Kaduna da aka sako, ya ce kullum sai masu garkuwa da su sun zane su sun kuma hana su yin Sallah a cikin daji.
Abdulganiyu Aminu ya ce idan lokacin Sallah ya yi sukan bukaci a bar su su yi, amma sai ’yan bindigar su hana su.
- An sake kai wa ofishin ’yan sanda hari a Imo
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 8 sun sace 28 a Kaduna
- Yadda na sauya akalar marigayi Ibro –Falalau Dorayi
- Za a dauki Kanawa 4,000 aikin dan sanda
“A tsawon mako uku dana yi a daji, ban yi wani isashshen barci ba, ta ya ma mutum zai iya yin barci? Saboda ba sa barin mu mu yi Sallah kuma kullum sai sun sa bakin bindigarsu sun doke mu,” cewar Aminu.
Matashin, bayan gwamnatin jihar ta damka su a hannun Hukumar Gudanarwar Kwalejin, ya bayyana cewa ’yan uwansa Haruna da Adamu na hannun ’yan bindigar har yanzu ba sako su ba.
Ya ce tun da ya zo duniya tsawon shekaru 25, wannan shi ne mummunan al’amari da ya taba faruwa da shi.
Aminiya ta gano dalibai biyar din da aka mika su ga hukumar gudanarwar Kwalejin su ne: Suzan M. Jatau, Ishaya Jafaru, Abdulganiyu Aminu, Haruna Aminud da kuma Adamu Amin.
Da yake jawabi, Kwamishinan Tsaron da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce Gwamnatin Jihar ta ji dadin samun karin mutum biyar da suka kubuta.
Ya kuma shawarci daliban, da su kasance masu juriya tare hana faruwar hakan wajen kawo musu nakasu ga harkar karatunsu.
Da yake karbar daliban a madadin shugaban Kwalejin, Dokta Usman Belli, ya gode wa masu ruwa da tsaki na jihar, da dukkan wanda suka taimaka wajen dawo da daliban.
Idan ba a manta ba, kashin farko na dalibai biyar da suka kubuta an mika su ga iyayensu, a Ma’aikatar Tsaro ta Jihar a ranar Laraba.
Bayan samun karin biyar da suka kubuta daga hannun ’yan bindigar, adadinsu ya kawo 10 ke nan.