✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kullum farautarmu ake kamar dabbobi – Shugaban Fulani

Shugaban kungiyar al’ummar Fulani ta Jamunati Fulbe da ke Kurmi, Alhaji Abdulkadir Salihu ya koka da yadda ake ta kashe al’ummarsa da shanunsu a kullum.…

Shugaban kungiyar al’ummar Fulani ta Jamunati Fulbe da ke Kurmi, Alhaji Abdulkadir Salihu ya koka da yadda ake ta kashe al’ummarsa da shanunsu a kullum.

Shugaban ya fadi a haka ne a yayin tattaunawarsa da Aminiya, inda ya ce an maida al’ummarsa kamar dabbobi, inda ake farautarsu, kamar kuma yadda ake alakanta su da kashe-kashen mutane da ke faruwa a sassa daban-daban na kasar nan.

Ya ce: “A yanzu mutane suna daukarmu a matsayin abokan gaba. Ana shafa mana kashin kaji, kan laifin da ba namu ba, ana daukarmu kamar masu laifi.”

Ya ce makiyaya a yankinsu, a kullum suna rasa shanunsu a sakamakon guba da ake sanya masu a wuraren da suke kiwo. Ya yi kira da cewa lallai ya kamata a gyara wannan al’amari, musamman domin a samu zaman lafiya.