✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kula da ciwon hawan jini

A wani rahoto da Jami’ar Edinburgh da ke Birtaniya ta fitar a makon jiya, ta ce mutum 1 cikin 4 na ’yan Najeriya zai iya…

A wani rahoto da Jami’ar Edinburgh da ke Birtaniya ta fitar a makon jiya, ta ce mutum 1 cikin 4 na ’yan Najeriya zai iya kamuwa da ciwon hawan jini. A cikin rahoton jami’ar ta ce adadin wadanda za su kamu da ciwon zai ci gaba da karuwa matukar ba a bi hanyoyin hana kamuwa da ciwon ba. Rahoton ya bayyana tuni ciwon ya zama ruwan dare game duniya a Najeriya, sakamakon kwaiwayon rayuwar mutanen yammacin duniya da ake yi a kasar nan.

Masana kiwon lafiya sun ce akalla fiye da mutum miliyan 20 ne suke fama da ciwon hawan jini a Najeriya a shekarar 2010, wanda hakan ya nuna ciwon ya kama namiji 1 cikin maza 3 da kuma mace 1 cikin mata 4 na ’yan Najeriya. Hakan ya sa aka kiyasta adadin wadanda za su kamu da ciwon zai kai miliyan 30 zuwa shekarar 2030.
Wani rahoto na daban ya ce kashi 10 cikin 100 na adadin wadanda suka kamu da ciwon a Afirka ta Kudu aka samu ikon kula da su.
Gungun masana na Jami’ar Edinburgh wadanda suka dauki nauyin bincike a kan ciwon hawan jini, inda aka buga rahoton a Mujallar ‘Journal of Hypertension’, sun ce rashin samun cikakken sunayen wadanda suke fama da ciwon a Najeriya da sauran kasashen Afirka ya sanya aka kasa fahimta yadda ciwon yake.
Dokta Dabies Adeloye malami a Jami’ar Edinburgh daya daga cikin wadanda suka gudanar da binciken a kan ciwon ya ce, sun gudanar da bincikensu a Najeriya ne ta hanyar bibiyar mutanen da suka kamu da ciwon a kasar, sun kuma yi hakan ne da fatan hukumomi da jami’an lafiya a kasar nan za su dauki matakan da suka dace wajen yaki da ciwon.
Ciwon hawan jini kamar sauran ciwuwwuka ne, idan har aka samar da hanyoyin wayar da kai da duba mutane da gano ciwo tun yana jariri da ciwon bai yawaita a kasar nan ba. Masanan da suka gudanar da binciken sun ce ba a dauki wadannan matakan a kasar nan ba.
“Idan aka kwatanta yadda ake kamuwa da ciwon a Najeriya da kuma kasashen gabashin a Afirka, a Najeriya ciwon ya ninka sau biyu, inda kashi 20 ciki 100 na ’yan Najeriya kadai suka fahimci suna dauke da ciwon. Ciwon hawan jini na haifar da matsala ga zuciya da koda da kuma haifar da shanyewar jiki.” Inji rahoton.
Rahoton ya ce a da ciwon hawan jini ya fi kama tsofaffi wadanda ake ganin damuwa ce ta haifar musu da ciwon, sabanin haka a yanzu matasa ma na kamuwa da ciwon, zai yi wahala a samu gidan da babu mai dauke da ciwon.
Idan ba a mayar da hankali wajen yaki da ciwon ba, ko kuma lura da shi yadda ya kamata ba, hakan zai haifar da shanyewar jiki.
Don haka ya kamata wannan rahoton ya tayar da tsimin hukumomi da malaman lafiya a kasar nan, su fahimci mawuyacin halin da ake ciki, sannan su samar da matakan kare kamuwa da ciwon. Matakan za su hada da samar da shirye-shiryen wayar da kan mutane dangane da alamomin ciwon da kuma matakan da za a dauka idan an kamu da ciwon.
Sannan ya kamata a rika hawa bene da kafa, ba wai a rika hawa na’urar hawa bene ba, a rika cin abinci mai kara lafiya, sannan a rika motsa jiki lokaci zuwa lokaci.
Mutanen da suke cin abinci a kantunan sayar da abinci ba su san da kayan hadin da aka girka abinci ba, wanda haka zai iya taimakawa wajen kamuwa da ciwon. Don haka ya kamata kantunan sayar da abinci su tabbata sun girka abincinsu da kayan hadin da suka dace, wadanda ba sa tattare da wata illa ga lafiya.
Ya kamata gwamnati ta samar da cibiyoyin lafiya da za a rika lura da masu hawan jini da kuma yin gwaje-gwaje don gano ciwon ko alamominsa.
Kiwon lafiya ya shafi kowa da kowa, don haka kowane dan Adam ya rika kaffa-kaffa da duk wani abu da zai kasance illa ga lafiyarsa, don haka jama’a su fahimci hanyoyin da za su kare kansu daga kamuwa da hawan jini.