✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kukan kauna

Wani saurayi ne da budurwarsa suna hira, sai ta ce masa tana jin kwadayi, ya je ya sayo mata gasasshen nama. Bayan ya fita sai…

Wani saurayi ne da budurwarsa suna hira, sai ta ce masa tana jin kwadayi, ya je ya sayo mata gasasshen nama. Bayan ya fita sai ya duba aljihunsa, ya ga Naira hamsin kadai yake da ita. Sai ya ce wa mai nama: “Ka ba ni nama na Naira hamsin amma ka yanka mini albasa da yawa.” Aka yanka masa ya kawo mata, dama an dauke wuta, akwai duhu, sai ya tura mata naman, shi kuma ya kama cin albasa. Nan fa idanunsa suka tara hawaye. Bayan lokaci aka kawo wuta, lokacin kuma suka gama cinye nama. Yarinya ta ga idon saurayinta na zubar hawaye, ta tambaye shi dalilin da yake kuka. Shi kuwa sai ya ce: “Tsananin kaunarki ce ta sanya ni kuka!”
Daga dan Fagge, 08058009561