✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kujerar shugaban Afirka ta Kudu tana rawa

A ranar Laraba ne Jam’iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta gudanar da wani taro na musamman a kan makomar Shugaban kasar…

A ranar Laraba ne Jam’iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta gudanar da wani taro na musamman a kan makomar Shugaban kasar Jacob Zouma.

Mulkin Shugaba Zouma na fuskantar zargi daban daban da rashawa da kuma sakaci wajen tabarbarewar tattalin arziki.

Jacob Zuma da ya yi ta kokarin kaucewa kokarin tsige shi a baya domin yana da karfi a jam’iyyar, amma a yanzu haka karfin shi ya ragu sosai tun bayan da jigogin jam’iyyar suka maye gurbinsa da mataimakinsa a matsayin shugaban jam’iyyar, wanda hakan ya san wasu rahotanni daga kasar ke nuni da cewa yana shirin amincewa da kiraye-kirayen da ake yi masa da ya yi murabus daga kan kujerar mulkin kasar, amma kuma wasu rahotannin suna nuna cewa ya ce zai amince ya sauka ne kawai idan shi ma aka amince da wasu bukatun da yake da su. 

A ranar Litinin da ta gabata, Jacob Zouma ya zauna da Sarkin Zulu, Goodwill Zwelithni, wanda shi ne shugaban gargajiya mafi girma a kasar Afirka ta Kudu.

Rahotannin sun nuna cewa gidan sarautar ta Zulu sun bukaci ya sauka cikin mutunci kamar yadda wani daga cikin ‘yan gidan ya shaida wa Jaridar Business Day, amma kuma a cewar majiyar, Zouma ya ki amincewa ya sauka inda yake cewa, “idan ya sauka ya zama kamar ya amince da zargin da ake masa ke nan na almundahana da cin hanci da rashawa.”

Ana sa ran sauraron babban jawabin kasa daga bakin Shugaban Jacob Zouma a kan makomar kasar da kuma makoyar siyasar kasar.

Tuni dai jiga-jigan jam’iyyar ta ANC suka juya wa Jacob Zouma baya inda suke ta kai ruwa-rana domin ganin shugaban ya mika mulki ga Ramaphosa, har ma sun taba tunkararsa da maganar a gidansa da ke Pretoria, inda ya yi watsi da bukatar ta su.

Su dai shugabannin Jam’iyyar ANC suna kokarin ne domin kawo karshen wannan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar ta hanyar dinke barakar da ta kunno kai a cikin jam’iyar domin kawar da rabuwar kai tare da kare martabarta domin su fuskanci zabe mai zuwa da karfinsu.