Wani kuduri da ke neman a daga likafar Kwalejin Ilimin Fasaha ta Tarayya (FCE) da ke garin Bichi a Jihar Kano zuwa matsayin jami’a ya tsallake matakin karatu ma biyu a zauren Majalisar Dattawa ranar Laraba.
Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta Arewa a Majalisar, Barau Jibrin ne ya dauki nauyin kudurin.
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 47 a Borno
- Zaben Mataimaki: Wike ya zama abokin takarar Atiku a PDP
Da yake gabatar da kudurin a gaban majalisar, Sanata Barau ya ce akwai bukatar a kara karfafa harkar ilimi ta hanyar sake kafa jami’o’in horar da malamai.
Ya ce idan kudurin ya zama doka, jami’ar, wacce za a rika kira da sunan Jami’ar Ilimin Fasaha ta Tarayya da ke Bichi, za ta taimaka wajen horar da kwararrun malaman da za a rika gogayya da su a duniya.
“Matukar muna so mu kawo sauyi a bangaren ilimin fasaha, muna bukatar irin wannan jami’ar. Za kuma ta kawo daidaito a harkar ilimi a Jihar Kano da ma Najeriya baki daya,” inji Sanata Barau.
Tuni dai kudurin ya tsallake matakin karatu na biyu a zauren majalisar.
Daga nan ne Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan, ya mika shi zuwa kwamitin Majalisar kan Manyan Makarantu don daukar mataki na gaba.
(NAN)