Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce Najeriya za ta sha mamaki ranar da yankin Kudancin kasar ya bayyana matsayinsa a kan zaben Shugaban Kasa na 2023.
Gwamnan ya kuma ce jam’iyyarsu ta PDP ba za ta yarda ta ba da tikitin takararta ga duk wanda zai mayar da hankali wajen kare muradun wasu tsirarun mutane ba.
Wike ya ce tuni wasu wadanda ba kasar ce a gabansu ba suka shiga yunkurin neman zama ’yan takarar.
A cewar wata sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan ya fitar ranar Asabar a Fatakwal, babban birnin Jihar, Gwamnan ya yi wadannan kalaman ne yayin wata liyafar girmamawa da ’yan kabilar Kalabari suka shirya a Karamar Hukumar Asari Toru da ke Jihar.
Ya ce, “Duk ranar da Kudu ta yi magana, Najeriya sai ta girgiza. Mun yi amanna da hadin kan kasar nan da ci gaba da kasancewarta kasa daya. Amma babu wanda zai yi mana barazana, dole Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya.”
Wike ya kuma ce ’yan kalilar ta Kalabari suna son junansu sannan suna da matukar hadin kai.
Yayin walimar dai, an karrama Gwamnan da sarautar Se-Ibidokubo na Kalabari.