Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce sun mayar da kudin bayar da takardar mallakar fili (C-of-O) a birnin Naira miliyan biyar.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da kungiyar masu gina gidaje ta Abuja, a ranar Talata.
- ‘Dalilin da muka lakada wa alkali duka a Gombe’
- Kotu ta sake bayar da belin Emefiele kan miliyan 300
Wike ya ce za a iya biyan kudin daga wata hudu da ba mutum filin, inda bayan nan ne za a damka wa wanda ya nema takardar.
Ministan ya kuma ce zai nemi amincewar Shugaban Kasa Bola Tinubu domin haɗa Lambar Shaidar Zama ɗan Kasa (NIN) da takardar kafin a ba mai neman ta.
Wike ya kuma ce lokacin da za a ba mutum uku ko sama da haka fili ta hanyar amfani da takardar bogi ya wuce.
“Idan muka yi abin da ya dace, wasu mutanen za su yi farin ciki, wasu kuma ba za su yi ba. Wasu masu hannu da shuni za su yi watsi da wasu tsare-tsarenmu, amma duk abin da zai taimaki mutanenmu, shi za mu yi,” in ji Wike.
Ya kuma yi alkawarin tabbatar da tsari da bin ƙa’ida wajen tsarin bayar da filayen a Abuja.