Wani likita Duste Musa, ya koka da kashe ɗaya daga cikin ’ya’yansa da masu garkuwa da mutane suka yi a jihar Kaduna.
Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga suka yi garkuwa da Janet Galadima, matar likitan, wacce ke zaman alƙalin kotun gargajiya a Kaduna, tare da ’ya’yansa maza huɗu.
An sace su ne a harin da aka kai gidansu da ke Mahuta New Extension, Ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna, a ranar 23 ga Yuni, 2024 da ƙarfe 11 na dare.
Bayan haka masu garkuwa da mutane sun nemi kudin Naira miliyan 300 amma aka kasa samun kuɗin.
Sakamakon haka, ‘yan fashin sun kashe dan likitan mai shekara 14 tare da yin barazanar kashe wasu idan ba a biya kudin ba.
Da yake zantawa da Aminiya, Likitan ya ce, “Na ɗauki ƙaddara daga Allah kuma ina roƙon Allah Ya sako matata da sauran ’ya’yanmu uku.”
Da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna ranar Laraba, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya, reshen Kaduna, Godwin Ochai, ya yi kira da a ceto iyalan likitan cikin gaggawa.
“Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Kaduna ta samu labarin sace ta Alƙaliyar da ’ya’yanta huɗu.”
“Wannan sabon salo na sace-sacen mutane da ake kai wa alƙala hari abu ne na Allah wadai, kuma yana neman a gaggauta ɗaukar mataki don jami’an tsaro su daƙile matsalar.
“Yawaitar sace-sacen jama’a a jihar na nuni da buƙatar ɗaukar matakin gaggawa daga gwamnati fiye da yadda suke yi a baya.”