✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kudin da muke ba wa ’yan sanda ya fi na Gwamnatin Tarayya —Gwamnoni

Fayemi ya ce gwamnoni na saya wa ’yan sanda makamai da motoci, duk da cewa a wasu jihohi babu kudaden 'Security Vote'

Gwamnoni sun yi ikirarin cewa suna saya wa ’yan sanda makamai sannan kudaden da suke kashewa a kan ’yan sanda a jihohinsu ya fi wanda Gwamnatin Tarayya take ba wa ’yan sandan.

Wannan ikirari ya fito ne daga Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, a lokacin wani taron tattauna da kungiyar gwamnonin ta shirya tare da hadin gwiwar Cibiyar Ci Gaban Dimokuradiyya (CDD), a Abuja.

Fayemi ya bayyana wa taron cewa gwamnatocin jihohi ne suke saya wa ’yan sanda makamai da motocin aiki tare da biyan su kudaden alawus, duk da cewa, “Wasu jihohin ba ma su da kudaden Security Vote da ake warewa domin ko-ta-kwana.”

Ya ce ya samu wannan bayani ne a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.

Gwamnan na Ekiti ya ce, “Da wuya a samu wata daga cikin hukumomin tsaro da kuke magana da ba ma kula da su muna ba su kudade; Kudaden da muke ba wa ’yan sanda sun fi wanda Gwamnatin Tarayya ke ba su. Wannan ba na shakka, a gaya wa duniya, ni ne na fada.

“Mun fi Gwamnatin Tarayya ba wa ’yan sanda kudade; Mu saya musu motoci mu biya su kudaden alawus, wani lokacin ma mu ke saya musu makamai, bisa doka.”

Fayemi ya bayyana cewa shigo da sojoji aikin yaki da matsalolin tsaro na cikin gida a jihohi 36 zai iya haifar da mummunan sakamako ga Najeriya.

Ya ce yin hakan ba daidai ba ne kuma karin nauyi ne da ake dora wa su sojojin a kan ainihin aikinsu na kare kasa daga barazanar tsaro daga kasashen waje.

“Mummunan abin da ba a so zai biyo baya, amma dai yanzu halin da muke ciki ke nan saboda yawancin ’yan Najeriya ba su aminta da ’yan sanda ba.

“Amma kuma idan ka sanya sojoji aiki a jiharka, abin da jihar za ta biya su kawai shi ne kudin cin abincin sojojin da ke wannan aikin.

“Duk da haka bai kamata a dora wa sojoji aikin da ba nasu ba ne, dora musu wani nauyi ne da bai rataya a wuyansu ba, saboda haka sai ka biya su.

“Shi ma wannan muna biya, muna kuma biyan ’yan Civil Defence. Babu wata hukumar tsaro a wata jiha da gwamnatocin jihohi ba su kula da ita fiye da Gwamnatin Tarayya , wadda ita ce alhakin kula da su ya rataya a wuyanta,” inji Fayemi.