Shugabannin Kungiyoyin addinin Kirista a Kudancin Jihar Kaduna sun kaurace wa taron da Hukumar Ziyarar Ibadar Kirista ta Najeriya (NPC) ta shirya domin magance rikicin yankin.
Shugabanin kungiyoyin sun bayyana hakan ne a sanarwa da shugbansu, Bishop Simon Peters Mutum ya fitar da ke zargin rashin sanar da manyan masu ruwa da tsaki a yankin da ya dade yana fama da kisan kare dangi, sai ’yan awanni kafin gudanar da shi.
Bishop Simon ya yi zargin cewa an riga an gama shirta taron ba tare da gudunmuwar masu ruwa da tsaki ba.
“Akwai mamaki a ce an shirya wa mutane taron zaman lafiya ba tare da tattaunawa da jagororinsu ba.
“Duk da cewa muna son shiga zaman tattaunawar, muna son sanin wawanda suka shirya shi da manufarsu, la’akari da yadda aka tsara shi.
“Muna kuma so mu san dalilin ware shugabannin SOKAPU, CAN da SKCLA wurin tsara taron”, inji sanarwar.
Tuni Kungiyar Jama’ar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta bukaci a dage taron, in ba haka ba ba za ta halarta ba.