Kotun daukaka kara kori karar da tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho na kasa, Abdulrasheed Maina ya daukaka, inda ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 8 da aka yanke masa kan karkatar da Naira biliyan 2.1 na ’yan fansho.
Kotun ta kori karar da Maina ya daukaka, yana zargin rashin ba shi damar kare kansa daga zargin da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a kai.
Sai dai kwamitin alkalai uku na kotun ya ce kotun farko ta ba shi damar kare kansa daga zargin, amma ya ki yi har lokaci ya kure, sannan ya gaza kawo kwararan hujjojin da za su wanke shi daga laifin.
A watan Nuwamban 2022 ne kotu ta yanke wa Maina hukuncin daurin shekara takwas kan karkatar da Naira biliyan 2.1 daga asusun kwamitin gyaran fansho da yake jagoranta.
Kotun ta ce za a fara lissafin shekara takwas din ne daga lokacin da aka fara tsare shi a shekarar 2019.
Ta kuma ba da umarnin rufe kamfaninsa mai suna Common Input Property and Investment Limited, a mallaka wa gwamnati kadarorin kamfanin.
A takardar karar da EFCC ta shiga, ta zargi tsohon shugaban gyaran fanshon da bude wasu asusun ajiya na bogi inda yake karkatar da kudaden.
Haka kuma ya rika amfani da wasu makusantansa da ke aiki a bankuna wajen wannan badakala, inda aka karkatar da Naira biliyan 1.5, da miliyan 500 da kuma wata miliyan 300 a lokuta daban-daban zuwa wadannan asusu.