Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tsarkake zukatan bayinSa masu takawa daga miyagun sha’awoyi da shubhohi. Ina gode maSa, godiyar wanda ya tabbatar da girmanSa da kamalarSa, ya kamfata daga kogin kyautarSa da falalarSa. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Makagin halittu, shaidawar da take jagorantar mai fadinta zuwa ga Aljanna. Kuma na shaida Shugabanmu Annabi Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda aka aiko zuwa ga dukkan halitta, Annabin da ya siffantu da mafiya kyan halaye da tsarkakan dabi’u, Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa.
Bayan haka, ya ku al’ummar Musulmi! Ko dayanmu ya taba tsayawa ya tambayi sirrin da ke cikin maimaita karanta Fatiha a cikin kowace raka’a ta sallolinmu na farilla ko nafila?
Jamhurun Malamai sun tafi a kan karanta ta rukuni ne daga rukunan Sallah. Shin kowane Musulmi yana kokarin sanin ma’anarta da bincike kan tafsirinta? Shin daliban ilimi suna kwadayi na musamman domin zurfafa sanin ma’anoninta? Don me ake karanta ta ga majinyaci-kan cutar ciki ko ta gaba- ta magance ta da izinin Allah kamar yadda ya tabbata a cikin Sahihaini daga Hadisin Abu Sa’idul Khudri (R.A), cikin kissar mutumin da kunama ta harba, inda ya mike tsaf lokacin da aka karanta masa ita, kamar wani abu bai same shi ba?
Wannan da sauransu ne, abubuwan da zan yi kokarin dubawa a cikin wannan huduba, mu tsaya tare mu nazarci wasu muhimman ma’anoninta.
Ku sani, kewaye mafi yawan ma’anoni da bin diddiginsu yana bukatar abubuwa biyu da ba su da na uku. Na farko samun tabbataccen ilimi. Na biyu daukar dogon lokaci.
Ku biyo ni, mu duba wasu daga cikin shiriyoyin da suke kunshe cikin wannan sura, da a kanta Manzon Allah (SAW) kamar yadda ya zo a Musnad da Tirmizi ya ce “Na rantse da wanda raina yake hannunSa, Allah bai saukar da kwatancinta ba a cikin Attaura ko Linjila ko Al-Furkan -Alkur’ani- ita ce Saba’ul Masani.”
Ibnu kayyim ya fada a cikin Midarajus Salikin, Mujalladi na 1 shafi na 74 cewa: “Allah Ya saukar da littattafai 104, Ya tattara ma’anoninsu a cikin Attaura da Linjila da Alkur’ani, kuma Ya tattara ma’anonin littattafan uku a cikin Alkur’ani, sannan Ya tattara ma’anonin Alkur’ani a cikin surori Mufassalai, sannan Ya tattara ma’anonin Mufassalai a cikin Surar Fatiha, sannan Ya tattara ma’anar Fatiha a cikin fadinSa “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in.” Ma’ana “Kai kadai muke bauta mawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa.” (k:1:5).
Malamai sun yi rubutu mai yawa kan tafsirinta har ma Imam Ibn kayyim (Rahimahullah) ya rubuta mujalladi uku yana bayani kan ayar “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in” kawai, a cikin mahsahurin littafinsa Midarajus Salikin baina Manazilu Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in.”
Imam Muslim ya ruwaito daga Abu Huraira (RA), ya ce “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Allah Madaukaki Ya ce, “Na raba Sallah gida biyu tsakaniNa da bawaNa, kuma bawaNa yana da abin da ya roka. Idan ya ce “Alhamdu lillahi Rabbil alamin.” Sai Allah Ya ce, “bawaNa ya gode miNi.” Idan ya ce “Arrahmanir Rahim.” Sai Allah Ya ce, “bawaNa ya yabe Ni.” Idan ya ce, “Maliki yaumiddin.” Sai Allah Ya ce, “BawaNa ya girmama Ni.” Idan ya ce, “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in.” Sai Allah Ya ce, “Wannan tsakaniNa da bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roka.” Idan ya ce, “Ihdina siradal mustakim. Siradal lazina an amta alaihim. Gairil magdubi alaihim wald dalin.” Sai Allah Ya ce, “Wannan na bawaNa ne, kuma bawaNa yana da abin da ya roka.”
Ya taron Muminai masallata! La’alla abin da ya gabata na tambayoyin da muka yi, ko kular da malamai suka ba surar, da abin da kuka ji na sahihan kalmomi da aka cisgo daga hasken Annabta game da wannan sura mai girma, su taimaka mana wajen kawar da gafala da mantuwa a cikin Sallah, al’amarin da masallata da dama suke kukansa a yau. Kuma kila tadabburin ma’anoninta ya kasance sababi na sanya tsoron Allah da khushu’i a zukatanmu, wanda shi ne ruhin Sallah, mu dandani zakinta mu gamsu da ita, ta yadda za a karba mana ita. Allah Ya datar da mu ga abin da yake daidai, kuma Ya shiryar da mu ga fahimtar nassoshin Sunnah da ayoyin Littafi (Alkur’ani).
“Alhamdu lillahi Rabbil alamin” Alhamd: Na nufin ambaton siffofin abin godiya ne tare da sonSa da girmama Shi, Rabbu, kuma shi ne Ubangiji Mai sarrafa al’amura. Rububiyya tana nufin umurni da hani ga bayi da saka musu kan kyautatawa ko munanawarsu. Duk da kasancewarSa (Allah) Mamallakin komai, Mai iko a kan komai da wani abu ba ya gagararSa, duk da haka Shi (Allah) Mai rahama ne, Mai jin kai. Don haka ka natsu ya kai Musulmi! Ka yi farin ciki, ka yi alfahari da Ubangijinka da kake bauta maSa, domin Mai rahama ne Mai jin kai. Yana afuwa kuma Ya yafe, kuma Ya gafarta. Mai hakuri ne ba Ya gaggauta ukuba. Mai karimci ne, ba Ya rowa. Don haka ka yi gaggawar komawa gare Shi tare da tuba daga aikata zunubi.
Idan kana sujuda, yana nuni da kaskantar da kai da tawali’u, kuma wannan ne abin da za ka fi kusantar Ubangijinka da shi. Ka ci ribar wannan dama, mai yiwuwa ba za ta sake dawowa gare ka ba. Ka bayar da duk abin da kake da shi a wannan lokaci, ka bijirar da rayuwarka gare Shi, kana mai tsoron azabarSa, mai kwadayin afuwarSa da yafewarSa. Shi Ya cancanta a bi Shi da takawa, kuma Ya cancanta ga Ya yi gafara.
A kowace raka’a mai Sallah yana karanta “Maliki yaumid din.” Mene ne “yaumid dini” da Allah Ya kebance shi da mulki, alhali Shi ne Mamallakin komai? Lallai surar Fatiha tana kunshe da ma’anar “Yaumid dini”, (Ranar Sakamako), tana tunatarwa game da ita. Rana ce da ba makawa kowane mutum sai ya halarce ta. Ayar “Maliki yaumid dini” tana farkar da mutum, kan ya dauki guzurin tafiyar da ba makawa ga kowane mai rai! Kuma gwargwadon karfin azama da karancin gazawarsa ne zai kasance irin tattalinsa ga wannan rana. Wannan rana ce ta alkawari da cika alkawari, rana ce ta shiga Aljanna ko wuta! Ranar da mutane za su gan su sun firfito daga kaburburansu suna masu kankan da kai, don amsa kiran Mai mulkin gaskiya! A lokacin Mala’iku sun sassauko daga sammai sun kewaye su, Ubangiji Ya bayyana a kan KursiyinSa, kasa ta haskaka da haskenSa, an aza Littafi, an zo da Annabawa da masu bayar da shaida, an kafa mizani, littattafan ayyuka suna watsuwa, an tattaro masu husuma, kowane mai bin bashi ya cakume wanda yake bi bashi, ga kishin ruwa, ga zafin rana… ga…! Sai a aza gada a kan tsurar wutar Jahannama domin tsallakewa ta kanta, wuta tana gauka tana cin sashinta a karkashin gadar, masu fadawa cikinta sun ninninka wadanda za su tsallake! (Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!)
Wajibi ne wadannan abubuwa su rika zuwa ga tunanin wanda ya tsaya domin yin Sallah, musamman a lokacin da ya karanto, “Maliki yaumid din,” ta haka sai ya dusashe kaifin ta’allaka da duniya ko karkata gare ta, domin ya yi fiffika zuwa Lahira.
A lokacin da kake cikin wannan yanayi kamata ya yi zuciyarka ta cika da tsoro, ba abin da ta mallaka face tawussuli zuwa ga Ubangijinka, ta yin addu’ar Ya shirye ka zuwa ga Tafarki Madaidaci. Ya taimake ka, Ya datar da kai, Ya budada kirjinka ga bauta maSa Shi kadai, domin ka tsira daga wahalhalun wancan Rana Mai girma da kaskancin da ke cikinta, ka rabauta da AljannarSa da samun yardarSa!
Dukkan wadannan ma’anoni da mafi yawan sigogin da suka shafe ta, da suka fi yin bayani suna nan a cikin ayar da ke bin wadda ta gabata, watau fadinSa Madaukaki: “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in.” Bambancin lafazin “Wa iyyaka nasta’in” da lafazin “Nasta’inuka” shi ne lafazin “nasta’inuka” yana iya zama “muna neman taimakonKa tare da waninKa,” amma lafazin “Wa iyyaka nasta’in,” na nufin “ba za mu nemi taimako ba sai daga gare Ka kadai, domin dukkan al’amura a hannunKa suke Kai kadai. Wani ba ya mallakarsu tare da Kai, koda misalin kwayyar zarra!” Wannan na nuna cewa, ba ya halatta a dogara da kowa, sai wanda Ya cancanci a bauta maSa, domin waninSa bai mallaki komai ba. Don haka kada ka dogara da shi ya kai Musulmi! Alakar da ke tsakanin ibada da tawakkali a fili take, kamar yadda wasu ayoyi suka bayyana cikin fadinSa Madaukaki: “Saboda haka ku bauta maSa kuma ku dogara gare Shi.” (k:11:123), da fadinSa: “To idan sun juya, sai ka ce: Ma’ishina Allah ne. Babu abin bautawa da gaskiya face Shi. A gare Shi nake dogara.” (k: 9: 129), da fadinSa “Ka ce, Shi ne Mai rahama, mun yi imani da Shi, gare Shi muka dogara.” (k:69:29), da sauransu.
Ibnu Taimiyya (Rahimahullahu), ya ce: “Iyyaka na’abudu” tana tunkude riya, “Wa iyyaka nasta’in” kuma tana tunkudi girman kai.”
Allah Ya amfanar da mu da shiriyar LittafinSa da Sunnar ManzonSa da ta Sahabbai, ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah a gare ne da ku.
Ku zo mu nazarci Ummul kur’an (1)
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tsarkake zukatan bayinSa masu takawa daga miyagun sha’awoyi da shubhohi. Ina gode maSa, godiyar wanda ya tabbatar da…