Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya buƙaci a riƙa tona asirin malaman tsubbu a duk inda suke.
Sarkin wanda shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, ya buƙaci malaman Musulunci da su riƙa fallasa duk masu fakewa da rigar malumta suna ayyukan tsubbu.
Basaraken ya buƙaci malaman addini da “su tsaftace harkar tasu, tare da tona asirin ɓata-garin cikinsu ga jami’an tsaro kafin miyagun su kai ga aikata munanan ayyukansu ko halaka jama’a.”
Ya yi wannan kira ne bayan kisan gillar da wani mai iƙirarin malumta mai suna Abdurrahman Bello, ya yi wa wata ɗaliba ’yar ajin ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ake Ilori, mai suna Hafsah Lawal.
A cikin sanarwar da basaraken ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Abdulazeez Arowona, a ranar Lahadi, ta umarci “malaman addini musamman limaman masallatan da ke Masarautar Ilori da ma faɗin Jihar Kwara, da su karkatar da huɗubobinsu kan inganta tarbiyya da kuma muhimmancin kare ran ɗan Adam, ba tare da la’akari da addini ko ƙabilanci ba.”