An zaga gari da wani mutum tsirara bayan an kama shi da tsakar dare bisa zargin tsubbace-tsubbace a jihar Kuros Riba.
An kama mutumin wanda ake zargi babban Fadan wani coci ne yana binne kayan tsafi ne a gidan wani mutum a garin Itigidi da ke Karamar Hukumar Abi.
Aminiya ta jiyo daga majiyar da ta bukaci kar a ambaci sunanta cewa asirin wanda ake zargin ya tonu ne sadda “ya bi dare yana binne kayan tsafi, ashe wasu suna ganinsa, daga cikin wadanda suka gan shin wani ya gane shi ya kuma san shi”.
“An zagaya gari da ‘faston’ a huntunsa kowa ya gan shi domin hakan ya zama darasi ga na baya masu miyagun hali irin nasa”.
- Matsafa sun yi wa tsohuwa yankan rago
- NCDC ta kora dalibai gida a Kuros Riba
- Sojoji sun kama ‘yan kungiyar asiri 61 a Kuros Riba
Bisa al’adar mutanen yankin idan aka kama mutum ya aikata abin kunya ana tube shi ne tsirara a zaga gari da shi kowa ya gan shi.
To sai dai matakin hukunta mai laifi bisa tafarkin al’ada na da hadari domin wasu maimakon su yi nadama su tuba kara tsunduma ma aka ce suke yi. Wasu kuma sauya gari suke yi su bar gida har abada domin sun bar wa ‘ya’ya da jikoki abin fada.
Ya zuwa lokcin rubuta wannan labarin Irene Ugbo, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kuros Riba ba ta amsa kiran yawa da wakilin mu ya yi mata ba. Hatta sakon kar-ta-kwana da aka aike mata game da lamarin ba ta mayar da amsa ba.