Fassarar Salihu Makera
Huduba ta Farko
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya saukar da Alkur’ani Mai girma a kan ManzonSa Muhammad (SAW) a cikin watan Ramadan inda Yake cewa: “Watan Ramadan ne wanda aka sauka da Alkur’ani a cikinsa…” Kuma Ya fifita shi a kan sauran watanni kamar yadda Ya fifita Alkur’ani a kan sauran Littattafai. Kuma Ya ambaci muhimmancin azumi ga al’ummar Mustafa (SAW) a cikin fadinSa: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke a gabaninku, tsammaninku za ku yi takawa. Kwanuka ne kidayayyu…” Sa’annan Ya yi sauki ga marar lafiya da matafiyi da tsoho da tsohuwar da suka manyanta da makamantansu a cikinsa. Allah Madaukaki Ya ce: “Wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, (sai ya biya) adadi daga wadansu kwanuka na daban. Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala (saboda tsufa ko wata cuta) akwai fansa; su ciyar da mataulaci, sai dai wanda Ya kara alheri, to, shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) shi ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani.”
Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a bisa mafificin halittar Allah, Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ina yi muku wasiyya da ni kaina da jin tsoron Allah Mabuwayi, Mai yawan gafara. Kuma ina kwadaitar da ku wajen yi wa Allah da’a da yi wa ManzonSa (SAW) da’a da kuma yi wa ma’abuta al’amari (shugabanni) daga cikinku da’a a cikin alheri ba a cikin sabo ba. Domin ba a biyayya ga wani abin halitta a cikin saba wa Mahalicci. Kuma ina tsoratar da ku game da saba musu a cikin magana ko aiki, a asirce ko bayyane, cikin dare ko rana a zaune ko a halin tafiya. Domin Allah Madaukaki Yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi wa Allah da’a kuma ku yi wa Manzo da’a da kuma ma’abuta al’amari (shugabanni) daga cikinku.” Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, hakika ya bace, bacewa bayyananniya.”
Ya ku bayin Allah! Ku tausaya wa junanku a cikin wannan wata mai albarka, domin Allah Mai jin kai ne. Kamata ya yi sashinku ya taimaki sashi da abinci ko abin sha ko dukiya ta halal ko matsuguni (gida) ko tufafi masu kyau. Kuma ku sadar da zumunta ko sulhunta a tsakanin Musulmi da sauran ayyuka na taimakekiniya da Musulunci ya tsara, kuma Annabinmu Muhammad (SAW) ya umarce mu da aikata su.
Ya ku bayin Allah! Ku guji zalunci, domin Allah Madaukaki Ya sanya shi abin haramtawa a tsakaninmu, don haka kada ku yi zalunci, kamar ku yi bulala ga kananan yaranmu ko ku bugi duk wanda kuka hadu da shi a kan hanya ba tare da hakki ba, ko ku kone abinci ko abin amfanin mutane, ko ku fitar da su (ku rushe) daga gidajensu ko ku ci dukiyarsu ku sadar da ita zuwa ga masu mahukunta (rashawa) da zalunci, ko ku kone amfanin gona da kashe manya da yara.
Ya ku bayin Allah! Ku guji kowane zalunci da fasadi, kuma ku tuba zuwa ga Allah, Allah Mai yawan karbar tuba ne Mai jin kai, gabanin Ya yi fushi da ku, idan kuka ki yin haka, to ku sani lallai Allah Mai tsananin ukuba ne.
Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah Mai girma gare ni da ku, ku nemi gafararSa Lallai ne Shi Ya kasance Mai yawan gafara ne.
Huduba ta Biyu:
Godiya da taslimi.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ku ji daga gare ni, kuma ku kiyaye abin da nake gaya muku, ku hankalta da shi, kada ku yi watsi da shi a bayan bayanku. Ku sani lallai azumin Ramadan ba ya inganta kuma bai kasancewa abin karba a wurin Allah Madaukaki, sai ya kasance a bisa yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar mana. Don haka ba ya halatta ga Musulmi baligi, mai hankali, namiji ko mace ya azumci wannan wata mai albarka ba tare da sanin abin da ke gyara shi da bata shi ba.
Ya ku bayin Allah! Kada ku yi girman kai wajen neman ilimi, saboda kuna da dukiya ko mulki ko matsayi ko kyakkyawar mace ko saboda kunya ko ’ya’ya. Domin Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Neman ilimi farilla ne (tilas) a kan Musulmi namiji da Musulma mace.” Muslim ya ruwaito.
Don haka ya ku bayin Allah! Ku sani lallai ne Allah Madaukaki ba Ya karbar ibadar mai ibada jahili murakkabi, wanda bai san yadda ake wankan janaba ba, ko alwala ko Sallah tare da karatun Fatiha da makamantan haka. Allah Madaukaki Yana fadi a cikin Hadisin Kudisi cewa: “Ku san Ni, kafin ku bauta Mini, idan ba ku san Ni ba, ta yaya za ku bauta Mini?”
Ya Ubangiji! Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka kaskantar da shirka da mushirikai. Ka darkake makiyanKa kuma makiya addini. Ka taimaki bayinKa masu kadaita Ka. Ya Ubangiji! Ka taimake mu taimako mabuwayi, Ka yi mana budi budi mabayyani.
Ya Ubangiji! Kada Ka bar mu da wani zunubi a wannan masallaci namu face Ka gafarta shi, ko wata damuwa face Ka kwaranye ta, ko bashi face Ka biya shi, ko kuntatacce face Ka saukaka maSa, ko makiyi face Ka kunyata shi, ko mai dukiya face Ka sanya masa albarka, ko fakiri face Ka wadata shi, ko masani face Ka yi masa ilhama (da alheri), ko jahili face Ka sanar da shi, ko mamaci face Ka yi masa rahama, ko daurarre face Ka kwance shi, ko mujahidi a tafarkinKa face Ka taimake shi.
Ya Ubangiji! Ka yi salati ga Annabi Muhammad da alayen Annabi Muhammad, Ka yi albarka ga Annabi Muhammad da alayen Annabi Muhammad, kamar yadda Ka yi salati da rahama da albarka a kan Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim. Lallai ne Kai Abin godewa ne Mai girma.
“Lallai Allah Yana yin umarni da adalci da kyautatawa da bai wa ma’abucin zumunta (hakkinsa), kuma Yana hani ga alfasha da abin ki da rarrabe kan jama’a. Yana yi muku gargadi, tsammaninku, kuna tunawa.” Ku tuna Allah, Ya tuna da ku, ku gode maSa a bisa ni’imominSa Ya kara muku, ku roke Shi Ya amsa muku, kuma ku nemi gafararSa, lallai Shi Mai yawan gafara ne.