Huduba ta farko
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, muna neman taimakonSa da gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmmu da munanan ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiyar da shi babu mai batar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu
bawan Allah ne, kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da Sahabbansa har zuwa ranar tashin kiyama.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Yana daga cikin abin da aka samu daga Manzon Allah (SAW) ya kasance mai yawan kyauta ne, kuma ya kasance yana kara yawan kyautar a cikin watan Ramadan, kamar sakakkiyar iska. karkashin wannan siffa ta kyauta ta Manzon Allah (SAW) na sanya wannan hudubar ta kasance a kan ciyar da marayu da talakawa, kuma manufa ta biyu ita ce yadda marayu suke karuwa a garuruwan Musulmi a yankin Arewa da kuma yadda talauci yake karuwa dare da rana.
Wannan karuwar marayu na faruwa ne sakamakon kashe- kashen da ake yi na dubban mutane wadanda suke barin ’ya’ya da mata da babu mai kula da su, kuma gajeren binciken da muka gudanar yana nuna cewa mawadatan Arewacin Najeriya za su iya tallafa wa wadannan marayu ba tare da wani ya ji labari ba cikin abin da Allah Ya azurtasu da shi. Allah Madaukakin Sarki Ya ce “Su ji tsoro wadanda suke barin ’ya’ya a bayansu raunana, wadanda suke ji musu tsoron talauci…”
’Yan uwa Musulmi! Yadda al’amarin yake dukiyar da Allah Ya ba mutum takan zama bala’i a gare shi idan bai fitar da zakkarta ba da sadakanta. Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Ku yi imani da Allah da ManzonSa kuma ku ciyar da abin da Allah Ya ba ku ajiyarsa, wadanda suka yi imani daga cikinku, suka ciyar suna da lada mai girma.”
Ya ’yan uwa Musulmi! Yana daga cikin cikakkiyar siffar mumini ta asali ciyar da dukiya, Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Wadanda suka yi imani da gaibi, kuma suke tsaida Sallah, kuma cikin abin da Muka azurtasu masu ciyarwa ne.” Bakara.
Kuma mai fadi zai iya cewa ai Allah Yana da ikon Ya ciyar da talaka ba tare da Ya nemi mawadata su ciyar da shi ba. Lallai haka al’amarin yake, amma Allah Ya yi haka ne don Ya jarabci mawadata da talakawa.
Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Idan aka ce musu su ciyar daga cikin abin da Allah Ya azurta su da shi, sai kafirai su ce da wadanda suka yi imani, za mu ciyar da wanda Allah idan Ya so zai ciyar da shi? Ku ba komai kuke ciki ba sai bata mabayyaniya.”
Duk wanda ya yi irin wannan furuci, to ya sani irin furuci ne na kafirai. ’Yan uwa Musulmi! Ya wajaba a kan mawadata su rika ciyarwa irin wadda ta dace, domin al’adar mawadata a Najeriya ta kasance ba sa ciyarwa sai in da za a gani, ko kuma su rika ba manyan malamai wadanda ba su da bukatar irin wannan taimako, suna yin haka ne don jahilci ko kuma domin riya, sai ka ga sun bar makwabtansu da ’yan uwansu na kusa a cikin yunwa da kuncin rayuwa, amma sun kai nesa.
Allah Maadukakin Sarki Ya ce: “Suna tambayarka me za su ciyar, to, ka gaya musu duk abin da suka ciyar na alheri yana komawa ne ga iyayenku da makusantanku da marayu da talakawa da matafiyi, kuma duk abin da kuka yi na alheri Allah Yana sane da shi.”
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, muna neman taimakonSa da gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmmu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah Ya shiyar da shi babu mai batar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu
(SAW) bawan Allah ne, kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa har zuwa ranar tashin kiyama.
Ya ’yan uwa Musulmi! Mutum ba ya tabbata a wannan duniya, mutum zai rayu ne iya ajalinsa, duk abin da aka ba mutum na dukiya bai yi aiki da ita ta hanyar alheri ba, to babu shakka ranar mutuwarsa sai ya yi nadama a lokacin da nadamar ba ta da amfani.
Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Ku ciyar daga abin da Muka azurtaku, tun kafin mutuwa ta zo wa dayanku, sai ya ce: “Ya Ubangiji dama Ka jinkirta mini lokaci kadan domin na yi sadaka kuma na zamanto cikin mutane na kwarai, kuma Allah ba Ya jinkiirta wa wata rai idan ajalinta ya zo…”
Ya ’yan uwa Musulmi! Ba sharadin ciyarwa ba ne mutum ya zama mawadaci, zai ciyar ne gwargwadon abin da Allah Ya ba shi. Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Mawadaci ya ciyar daidai karfinsa, wanda Allah Ya takaita (kuntata) masa arzikinsa ya ciyar iya abin da Allah Ya ba shi.”
Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Allah ba Ya dora wa wata rai (nauyin ciyarwa) sai abin da Ya ba ta.”
Manzon Allah tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi ya ce: “Ku kiyaye kanku daga wuta koda da rabin dabino ne, wanda bai samu ba, to ya yi da kalma mai dadi.”
Kuma mu sani ’yan uwa kyauta siffa ce ta mutanen kirki masu alheri, rowa kuma siffa ce abar zargi a wurin Allah da ManzonSa (SAW) ga mai aikata ta.
Ka sani ya kai bawan Allah! Dukiyarka ta asali ita ce wacce ka yi kyauta ko sadaka da ita, amma wadda ka yi tufafi da ita za ta lalace, wadda ka ci kuma za ta rube, wadda ka tara ba ka yi amfani da ita ba za a yi maka hisabi kanta ranar tashin kiyama.
Ya ku bayin Allah! Yana daga cikin abin da ya wajaba a kan hukumomin wannan kasan tun daga kananan hukumomi har zuwa ta tarayya, su kula tare da tallafa wa marayu, domin adadinsu yana karuwa, sakamakon fitintinun da ake samu a wannan kasa da tashin bama-bamai, kuma ya wajaba a kan wadanda ake damka hakkin marayu a hannunsu, su ji tsoron Allah su rika isar da hakkokin masu shi zuwa gare su.