✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku rika fallasa masu yi wa ’ya’yanku fyade —Matar Gwamnan Gombe

Matar Gwamnan Jihar Gombe, Asama’u Yahaya, ta yi kira ga iyayen yara da su daina yin shuru suna kyalewa idan aka yi wa ’yan’yansu fyade…

Matar Gwamnan Jihar Gombe, Asama’u Yahaya, ta yi kira ga iyayen yara da su daina yin shuru suna kyalewa idan aka yi wa ’yan’yansu fyade ko wani cin zarafi.

Hadimar gwamnan jihar kan sha’anin yada labarai, Bintu Sunmonu ta ce Hajiya Asma’u ta ce iyaye su daina bata lokaci wajen kai rahoto ga hukuma a duk lokacin da irin wannan matsalar ta faru.

Matar Gwamnan ta yi amfani da wannan dama wajen yaba kokarin Majalisar Dokokin Jihar na tabbatar da Dokar Hana Cin Zarafin Mutane (VAPP) a jihar.

A ranar 18 ga Oktoba Majalisar ta amince da wannan sabuwar doka.

Majalisar ta amince da dokar ne bayan gamsuwa da rahoton kwamiti na musamman da ta kafa kan harkokin shari’ar jihar.

A cewar Hajiya Asma’u, a baya rashin dokar ya sa rayuwar mata a jihar na fuskanatar kalubale, ba tare da hukunta masu cin zarafinsu yadda ya kamata ba.

Da wannan cigaba da aka samu, Jihar Gombe ta shiga jerin jihohin da duk wanda ya taba mutunci mace ba zai ji da dadi ba.