Hukumar bunkasa fitar da kayayyaki ta Najeriya (NEPC), ta yi kira ga masu matsakaitan sana’o’i da su yi mafani da dabrun kasuwanci na zamani wajen sayar da kayayyakinsu ga kasashen waje.
Babban Daraktana Hukumar, Dokta Ezra Yakusak ne ya bayyana hakan a taron wayar da kai ga masu ruwa da tsaki na Arewa maso Gabashin Najeriya kan kasuwancin zamani.
- Yadda aka yi ruwan zallar kankara a Taraba
- Amurka za ta taimaka wa Najeriya magance matsalolin yanayi
Daraktan, wanda shugaban Hukumar na shiyyar, John Okorie ya wakilta, ya ce an shirya taron ne domin lalubo dabarun kawar da shingayen kasuwancin da ke sanya kasashen ketaren kin sayen kayayyakin da aka sarrafa a Najeriya.
“Muna fatan sabbin cibiyoyin kasuwancin da aka kaddamar a Najeriya za su taimaka wajen rage wa kasar dogara da kudin shiga na man fetur.
“Cibiyoyin sun hada da na Alkahira da Lome da Nairobi da aka kaddamar tsakanin watan Maris zuwa Agusta, kuma tuni sun fara aiki gaba daya. Wasu kuma za su biyo baya nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
A nasa bangaren shugaban sashen yada labarai na Hukumar a fannin kasuwanci , Friday Ogiri, ya ce an shirya taron bitar ne domin ilmantar da masu ruwa da tsaki game da muhimmancin samar da cibiyoyin, da kuma karfafa guiwar ’yan kasuwa kan muhimmancin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da kuma musayar kudaden tsakaninsu.