Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
Duk wanda ya karanta taken wannan rubutu kila abu na farko da zai fara tambayar kansa shi ne, shin dama mata suna yin walima ne ta aure a cikin shari’a? To amsar ita ce “’A’a”. Wani biki ne na musamman da aka kirkire shi daga baya aka kuma cusa shi cikin shagulgulan bikin aure da zummar hana daya ko biyu daga cikin bukukuwan da ake ganin su a matsayin ba daidai ba kuma sun yi hannun riga da shari’a. To sai dai bakon da aka raka tuni ya dawo. Abin da aka so a gujewa ba a iya guje masa ba har ma kara rincabewa lamarin ya yi.
Kafin in yi bayanin yadda walimar take ko kuma yadda ake yin ta da kuma hujjojina na rashin alfanunta da har ya sa nake son angaye su daina bata gishirinsu wajen dahuwar kaho a kanta, kai mai karatu ka sani akwai masu ganin wannan walimar da muhimmanci saboda a wajen yin ta, mata da yawa sukan karu da nasihohin da aka aiwatar a wannan rana, kuma ko ba komai an kashe yin taron kide-kide da raye-rayen da ake yi a lokacin aure. To kun ji tasu, ni kuma ga tawa a kasa.
A wuraren da ake yin walimar, daga cikin harajin ba gaira babu dalili da ake dorawa angaye akwai kudin wannan walimar, a cikin kudin ne za a yi sayayyar kayan abinci da kuma kama hayar wurin da za a zauna, haka kuma a ciki ne za a ware kudin da za a ba malamar da za a gayyato domin ta yi wa amarya gargadi da jan kunne akan sha’anin zaman aure. Sai a saka rana a gayyato abokai da ’yan’uwa domin su halarci wannan walimar, da ake cewa idan an je za a yi wa amarya hannunta mai sanda.
A ranar da za a yi wannan walimar, sai ’yan matan amarya su ci kwalliya, ita ma amaryar haka. Shigar da sukan yi ba bakuwa ba ce a cikin al’umma, domin duk wanda ya saba ganin shiga ta fitsara da tallar jiki da mataye ke yi a lokacin da suke yin bukukuwa, to ba ya da bukatar sai na gaya masa yadda shigar take. Sai dai kila in bai saba ganin walimar yadda ake yin ta ba, akwai bukatar in gaya masa hatta amaryar da ake yi wa walimar, a mafi yawancin lokuta, shigar da takan yi har ma takan dara ta kawayenta muni saboda yanayin sakin jikin da kuma matsewa. Wai a haka kuma, an zo ne domin a yi mata gargadi don ta ji tsoron Allah a cikin zamantakewar aure.
To idan an hallara a wajen da za a gabatar da walimar, a rabin lokaci na farko, malama ce za ta mike tsaye bayan an bude taro da addu’a, sai ta fara yin wa’azinta, wanda a mafi yawancin lokuta yakan karkata ne zuwa ga koyar da amarya yadda yakamata ta faranta wa mijinta rai musamman a wajen ibadar aure. Su kuma a nasu bangaren ’yan matan amaryar, a lokacin da malama ke wa’azi, sukan rabu gida uku ne, kashi na farko suna tsegumin malamar (Zan gaya maku me suke cewa daga baya), kashi na biyu kuma suna hirar gabansu suna masu jiran lokacin walimar ya kare a raba musu abinci su wuce gida, inda kashi na uku suke kasancewa abokan amarya ne da za su rika kai da kawo domin tarbo bakin da ke zuwa da kuma tabbatar da cewa kayan ci da na sha sun zama tsaf domin rabawa. Abin da nake son in ce a takaice ya kai ango, malama na wa’azi su kuma abokan amarya da amaryar suna shagalce wajen yin wani abu daban. A haka rabin lokaci na farko ke karewa.
Sai kuma rabin lokaci na karshe, akan gayyato iyayen amarya da gwaggwani da sauransu domin su yi wa ’yarsu fatan alkhairi, to a daidai wannan lokacin ne kuma ake fara raba abinci inda za a raba hankali gida biyu, wasu na yunkurin su karbi abinci su wuce, wasu kuma na yunkurin su yi hoto da amarya… a haka dai har a yi addu’ar rufewa wani bai ko san an yi ba. To kai ango daga nan an kashe maka Nairorinka na walima da ka bayar. Sai kuma idan Allah Ya kai rai gobe, sai kuma a yi ranar kawaye, ko ranar Fulani, ko ranar kauyawa da dai sauransu, shi ma bikin da akan raye (rawa) a saute ( da kide-kide), Allah Ya yafe mana baki daya.
To yanzu wannan walimar ina amfaninta yake? Walimar da rana daya bayan an gabatar da ita, wadannan mahalartan na jiya, su ne kuma za su koma taruwa domin sheke aya… Ai kai ango, ko ba domin ka ceci daraja da martabar addini da ake zubarwa a wannan ranar ba, ya kamata ka ceci aljihunka da sulallan da ke cikinsa. Amma dai ba mamaki, kila idan na fede maka biri har wutsiya akan abin da na rubuta a sama, za ka gamsu da ni ka yarda da cewa walimar ba ta da amfani kuma aibinta ya hau saman kashi 80 cikin 100. Amma mu hadu a rubutu na biyu.
Nasir Abbas Babi 08033186727