Shugaban Hukumar Ilimi a Matakin Farko a Jihar Sokoto, Shu’aibu Gwanda Gobir, ya gargadi malaman da ba su da asusun banki da cewa su gaugauta budewa ko su rasa albashinsu.
Ya ce gwamnatin jihar ba za ta amince da biyan albashin malamai ba a bisa tebur, kuma duk sakataren ilimin da aka kama yana yin hakan zai gane kurensa.
“Ku bude Asusun banki. Duk malamin da bai bude ba to ba za a biya shi albashin watan Yuli ba.” inji Gobir
Gobir, wanda ya nuna bacin ransa a wajen raba kayayyakin karatu ga kananan Hukumomi 23 na jihar, ya ce hukumar ta gaji da karbar korafin malaman na cewa ba su sami albashinsu ba.
Da ya ke nasa bayanin, Darakta mai kula da rarrabar kayayyakin hukumar, Kabiru Aliyu, ya ce an raba kayayyakin ne musamman ga wuraren karatu 1,420 da ba na boko ba.
Ya ce kayayyakin sun hada tufafin makaranta da jikkunan makaranta da allunan rubutu da dasta da ababen rubutu da kuma tabarmi.