✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ku ba Atiku shawara ya je gida ya huta, ya hakura da takara – Tinubu

Tinubu ya ce Atiku ya dade yana tsayawa takara yana faduwa

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a shawarci takwaransa na PDP, Atiku Abubakar, ya janye daga takarar da ya ke yi ta neman Shugabancin Najeriya saboda ba zai ci ba.

Tinubu, ya yi wannan kiran ne a fadar Oboro Gbaraum, wani basaraken gargajiya na masarautar Gbramatu da ke jihar Delta a yayin da ya kai masa ziyara ranar Juma’a.

A jawabin nasa mai cike da zambo, Tinubu ya yi ce ‘yan takarar shugabancin kasar kalilan ne suke da nagarta.

“Atiku ya dade yana tsayawa takarar zabe yana faduwa, wannan zaben ma ba zai kai labari ba, don haka ku ce mi shi ya je gida ya huta”.

“Daya dan takarar kuwa, gwani ne wajen bayar da alkaluman lissafi da kididdiga na karya… in ambaci sunansa a nan ma kaskanci ne a gare ni,” inji  Bola Tinubu a fadar basaraken.

Sannan ya kare jawabinsa da cewa, shi ne ya fi dacewa da mulkin Najeriya, don haka masarautar Gbaramatu ta zabe shi saboda shi ya san mafita ga matsalolin Najeriya.

Ya kuma yi alkwarin idan ya ci zabe sai rika shawartar masarautar kan duk wani batu da ya shafi ci gaban yankin, musamman wajen samar da aikin yi ga dinbim matasan yankin da sauransu.

%d bloggers like this: