Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Kano, Alhaji Tajo Othman, ya bayyana dalilin da mayar da rarar kuɗin kwangila har naira miliyan 100 zuwa asusun gwamnatin jihar.
A bayan nan ne dai Alhaji Tajo Othman ya mayar da kimanin naira miliyan 100 na rarar kuɗaɗen kwangilar ɗinka tufafin makaranta ga ɗaliban firamare dubu 789 a faɗin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.
Da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a a birnin Dabo, Kwamishinan ya ce ya yi hakan ne sakamakon tasirin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a kansa na zama jagora adali kuma abin koyi.
A cewarsa, bai taɓa tsammanin Gwamnan zai faɗa wa duniya ya mayar da rarar kuɗin zuwa lalitar gwamnatin ba, amma sai ga shi ya yi hakan a yayin ƙaddamar da rabon tufafin ɗaliban domin ya zama abin koyi ga al’umma su zama masu riƙe amana.
Kazalika, Kwamishinan ya ce a matsayinsa na shugaban kwamitin ɗinka tufafin ’yan makaranta a jihar, gwamnan ya danƙa masa amanar ganin ya sauke wannan nauyi cikin nagarta da adalci.
A makon nan ne aka riƙa yabon Kwamishinan bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa ya mayar da rarar kuɗaɗen da aka ware domin ɗinkawa daliban firamare sabbin tufafin makaranta,
Aminiya ta ruwaito cewa, kuɗaɗen da aka ware na kimanin naira biliyan biyu sun rara, inda Kwamishinan Tajo Othman bayan kammala aikin ya mayar da rarar zuwa asusun gwamnati.